Shirye-Shiryen Mika Mulki: Shugaba Buhari Da Bola Tinubu Sun Zaga Fadar Shugaban Kasa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Asiwaju Bola Tinubu sun zagaya gidan gwamnati don nunawa zababben shugaban kasar muhimman wurare a fadar shugaban kasar
- A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne Shugaba Buhari zai tattara kayansa tare da mika mulki ga Tinubu
- Shugabannin biyu sun zagaya ciki da wajen fadar shugaban kasar ne jim kadan bayan sun idar da sallar Juma'a
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zagaya da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu fadar shugaban kasa domin nuna masa muhimman wurare a yau Juma'a, 26 ga watan Mayu.
Sun gudanar da zagayen gabannin bikin rantsar da shugaban kasa wanda za a yi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Buhari da Tinubu sun zaga fadar Villa bayan sallar Juma'a
Shugabannin biyu sun dai yi zagayen ne jim kadan bayan sun idar da sallar Juma'a a masallacin gidan gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban jami'in hulda da jama'a na fadar shugaban kasar (SCoP), Ambasada Lawal Kazaure, ya gabatar da muhimman bayanai kan zagayen wanda ya fara daga zauren majalisa ta dakin taron manema labarai da sauran wurare a cikin fadar shugaban kasar.
Ma'aikatan fadar shugaban kasa da jami'an tsaro sun yi wa Buhari da Tinubu rakiya yayin zaiyarar sanin wuraren.
Osinbajo ya zagaya da Shettima fadar Villa
A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ma ya zagaya da zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima don nuna masa wurare a fadar ta Aso Rock, rahoton The Nation.
Aisha Buhari ta mikawa Remi Tinubu muhimman takardu na ofishin matar shugaban kasa
A baya mun kawo cewa matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta mika muhimman takardu na ofishin matar shugaban kasa ga Oluremi Tinubu, matar zababben shugaban kasa mai jiran gado.
An yi bikin mika mulkin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda Aisha ta mikawa Remi nauyin da ya rataya kan kujerar.
Aisha Buhari ta nuna jin dadinta kan damar da aka bata na gudanar da ayyukan taimakon jama'a da kuma hadin gwiwa da kungiyoyin agaji a tsawon shekaru takwas da ta yi a ofis.
Asali: Legit.ng