Dalilin Da Yasa Bai Kamata A Rantsar Da Tinubu A Ranar 29 Ga Watan Mayu Ba, Datti Baba-Ahmed Ya Bayani

Dalilin Da Yasa Bai Kamata A Rantsar Da Tinubu A Ranar 29 Ga Watan Mayu Ba, Datti Baba-Ahmed Ya Bayani

  • Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana rashin goyon bayansa kan rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima
  • Baba-Ahmed ya jaddada cewa rantsar da Tinubu wanda nasarar zaɓensa ba ta cika sharuɗɗan kundin tsarin mulki ba, tamkar kawo ƙarshen dimokuraɗiyya ne
  • Dan takarar mataimakin na jam'iyyar Labour, ya ce shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Mahmood Yakubu ya yi wauta da ya bai wa Tinubu takardar shaidar lashe zaɓe

Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce game da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Kwanaki hudu da suka rage a rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Najeriya, Baba-Ahmed ya sake nanata cewa rantsuwar za ta zama kamar saɓawa tsarin dimokuraɗiyya ne.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

Datti Baba-Ahmed ya bayyana dalilin da ya sa ba za a rantsar da Tinubu ba
Datti Baba-Ahmed ya bayyana dalilin da ya sa ba za a rantsar da Tinubu ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Yusuf Datti Baba_Ahmed
Asali: Facebook

Yusuf Datti ya bayyana abinda doka ta ce kan batun rantsuwar

Datti ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da zaɓaɓɓun sanatoci takwas da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai na tarayya 36 na jam'iyyar Labour a Abuja, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Datti ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da su ta manhajar Zoom. Ya bayyana cewa rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Tinubu, ka iya kai wa ga kashe dimokuraɗiyya a Najeriya.

Datti ya ƙara da cewa abin da yake shirin faruwa a ranar 29 ga watan Mayu, kwata-kwata ya saɓawa tsarin mulkin ƙasa ko ta yaya aka gudanar da shi.

Babban lauya ya bayyana abinda zai sa a rantsar da Tinubu duk da ana shari'a a kotu

Barista A.D Rotimi George ya bayyanawa Legit.ng cewa bikin rantsuwa na ranar 29 ga watan Mayu na da muhimmanci ba ga iya jam’iyya mai mulki kaɗai ba, har ma da al’ummar Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Gabatarwa Tinubu Aikin Farko Da Ta Ke Son Ya Yi Da Zarar Ya Shiga Ofis

Ya ce hakan zai share fagen bai wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu damar fara mulki tunda Buhari zai karkare a 29 ga watan Mayu.

George ya kuma ce korafe-korafen da aka shigar a kotu kan batun zaɓen shugaban ƙasa da Tinubu ya lashe a ranar 25 ga watan Fabrairu na ci-gaba da janyo muhawara.

Wasu na kira da a ɗage bikin rantsar da shi, wasu kuma na ganin cewa bai kamata a yi bikin rantsar da shi ba har sai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta gama yanke hukunci.

Sai dai gwamnatin tarayya ta dage kan cewa bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na nan babu fashi, inda ta ƙara da cewa shari'ar da ake yi ba za ta shafi bikin ba.

'Yan adawar da ake tunani Tinubu zai bai wa muƙamai

A wani labarin da muka wallafa a baya, mun kawo muku sunayen wasu 'yan jam'iyyun adawa da ake tunanin cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu zai basu muƙamai a gwamnatinsa.

Tun da farko Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙunshi kowa da kowa ciki kuwa har da 'yan jam'iyyun adawa da yake ganin za su kawowa gwamnatinsa ci-gaba wajen ayyukan da ta tasa gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng