Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Rusa Majalisar Kwamishinoninsa, Ya Sallami Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa

Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Rusa Majalisar Kwamishinoninsa, Ya Sallami Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa

  • Kwanaki kadan gabanin sake rantsar da shi, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya rusa majalisar kwamishinoninsa da sauran masu rike da muƙaman siyasa
  • Rushewar ta shafi shugabannin ma’aikatu da maƙarrabansu, ma’aikatu, hukumomi (MDAs) da kamfanonin gwamnati
  • Sai dai SSG, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da kuma sakataren gwamnan na musamman za su ci gaba da riƙe muƙamansu zuwa lokacin da za su ji wani umarni daga gwamnan

Bauchi - Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, ya amince da rusa majalisar zartarwa (SEC) ta jihar.

Mambobin majalisar da aka rusa sun haɗa da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da suka yi aiki ƙarƙashin gwamnatin a cikin shekaru huɗu da suka gabata.

Rusa majalisar dai na zuwa ne kwanaki kaɗan gabanin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023, a wa'adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Bauchi, in ji jaridar Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Zo da Sabon Tsari, Ya Umarci Kwamishinoni da Hadimai Su Bayyana Dukiyarsu, Ya Kore Su

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya rusa majalisar kwamishinoninsa
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya rusa majalisar kwamishinoninsa. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Gwamna Bala ya godewa kwamishinonin

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Barista Ibrahim Kashim ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron bankwana da majalisar zartarwa ta jihar ta gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar Bauchi a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Kashim a yayin taron, Gwamna Mohammed ya godewa ‘yan majalisar da ke barin gado bisa irin gudummawar da suka bayar wajen nasarorin da gwamnatinsa ta samu a wa’adinta na farko.

Ganduje ya rushe majalisar kwamishinoninsa

Kwanaki kaɗan ya kammala wa’adinsa na mulki, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, shi ma ya ba da sanarwar rushe majalisar kwamishinoninsa da sauran masu muƙamai.

Gwamna Ganduje ya umarci dukkan jami’an gwamnati da ke riƙe da muƙaman siyasa da su miƙa al’amuran ofisoshinsu kamar yadda yake a doka.

Umarnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar mai ɗauke da sa hannun babbar sakatariya, Hajiya Bilkisu Maimota.

Kara karanta wannan

29 Ga Mayu: Gwamnoni 5 Masu Barin Gado Wadanda Mai Yiwuwa Ba Za Su Miƙa Mulki Cikin Ruwan Sanyi Ba Da Dalilai

Ku ci-gaba da zama kan muƙamanku har ƙarshen mulki, Buhari ya gayawa ministoci

Shi kuwa a ɓangarensa, shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya shaidawa ministocinsa cewa su ci-gaba da zama a kan muƙamansu har zuwa ƙarshen mulkinsa.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja bayan kammala taron bankwana da majalisar ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Tags: