Tirƙashi: Kansiloli a Oyo Sun Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Har Sai Baba Ta Gani
- Kansilolin karamar hukumar Kajola ta jihar Oyo sun dakatar da shugabansu, Afolabi Salimonu har sai baba ta gani
- Kansilolin dai sun ce an dakatar da shugaban ne saboda yadda yake tafka kura-kurai da rikon sakainar kashi, da kuma karkatar da kuɗaɗen ƙaramar hukumar
- Shugaban ƙaramar hukumar bai ce komai ba dangane da dakatarwar da kansilolin suka yi masa
Majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kajola ta jihar Oyo, ta sanar da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar, Afolabi Salimonu, wanda aka fi sani da Borikansunwon, har zuwa abinda ya sawwaka.
Takardar dakatarwar da jaridar Punch ta samu ta bayyana cewa kansilolin sun dakatar da shugaban ne a yayin wani zama a zauren majalisar na sakatariyar ƙaramar hukumar.
Sun bayyana cewa matakin yana kan tsarin dokokin ƙasa da kuma dokokin majalisar jihar.
Dalilin dakatarwa
Kansilolin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon ganin yadda ake ƙara samun taɓarɓarewar abubuwa a ƙaramar hukumar saboda irin riƙon sakainar kashin da shugaban ke yi wa abubuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sannan sun zargi shugaban majalisar da karkatar da kuɗaɗe gami da yin almubazzaranci da dukiyar ƙaramar hukumar.
Sun kuma ƙara da cewar dakatarwar ta fara aikin ne nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba, kamar yadda Inside Oyo ta wallafa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar kansilolin, Adediran Tajudeen mai wakiltar mazaɓa ta biyu (Elero) ne ya gabatar da ƙudirin dakatarwar, a yayin da mataimakiyarsa Amusat Adebare mai wakiltar mazaɓa ta tara (Isia) ta mara masa baya.
Shugaban ƙaramar hukumar bai ce komai ba
Shugaban majalisar kansilolin, Ayegboyin Kehinde, mai wakiltar mazaba ta 8 (Isemi-Ile/Ilua)” ne ya jagoranci zaman majalisar.
Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, duk ƙoƙarin da aka yi na samun shugaban ƙaramar hukumar a waya ya gagara saboda baya ɗaga kiran da aka yi masa.
Shugaban ƙaramar hukuma ya lakaɗawa kansila dukan tsiya
A wani labarinmu na kwanakin baya, kun karanta yadda wani shugaban ƙaramar hukuma ya lakaɗawa ɗaya daga cikin kansilolinsa dukan tsiya a wurin taro.
Hakan dai ya samo asali ne daga wata 'yar hatsaniya da ta ɓarke a tsakaninsu kan wasu takardu da kansilolin suka buƙata daga shugaban karamar hukumar.
Asali: Legit.ng