Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Tony Blair
- Tsohon firaministan Burtaniya, Tony Blair, ya ziyarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a masaukinsa na Defence House
- Tony Blair ya ziyarci Bola Tinubu ne ana saura kwanaki kaɗan ya ɗare kan kujerar shugabancin ƙasar nan
- Tun bayan da aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, shugabannin ƙasashe da dama sun aike masa da saƙonnin taya murna
Abuja - Tsohon firaministan Burtaniya, Tony Blair, ya ziyarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ranar Talata a Defence House da ke birnin tarayya Abuja.
Ziyarar Blair na zuwa ne kwanaki shida kafin a rantsar da Bola Tinubu, a matsayin magajin shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari.
Tinubu ya bayyana ziyarar da Blair ya kawo masa cikin wata sanarwa a shafinsa na Twitter.
Sanarwar na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yau na karɓi baƙuncin tsohon firaministan Burtaniya kuma wanda ya kafa cibiyar Tony Blair Institute for Good Governance, Mr Tony Blair, a Defence House, birnin tarayya Abuja."
"Mun tattauna kan ɓangarori masu muhimmanci a gare mu da yadda Najeriya za ta ci gaba da amfani da aikin da cibiyarsa ta ke yi."
Channels Tv ta kawo rahoto cewa waɗanda suka halarci zaman, sun haɗa da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Shugabannin ƙasashe da dama sun taya Tinubu murna
Tun lokacin da aka bayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, shugabannin ƙasashe da dama, ciki har da firaministan Burtaniya, Rishi Sunak, sun aike masa da saƙonnin taya murna.
A ranar Talata da ta gabata, sakataren fadar gwamnatin Amurka, Anthony Blinken, ya kira Tinubu a waya, inda ya ƙara jaddada aniyar Amurka ta ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka, a mulkin Bola Tinubu.
Amurka Ta Zabi Jami’an Gwamnati 9 da Za Su Halarci Bikin Rantsar da Tinubu a Abuja
Rahoto ya zo kan yadda ƙasar Amurka ta zaɓo wasu muhimman wakilanta waɗanda za su halarci bikin rantsar da Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin shugaban ƙasa.
Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, ya aike da tawagar sunayen mutum tara.
Asali: Legit.ng