Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai karbi ragamar mulkin Najeriya ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan wa'adin shugaba Muhammadu Buhari ya cika.
Premium Times ta ce lokacin da yake fafutukar neman zama shugaban ƙasa, Tinubu ya ƙulla kawance da manyan 'yan siyasa a ƙasar nan ciki harda mambobin jam'iyyun adawa.
Bayan lashe zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023, Tinubu ya yi kira da a haɗa gwamnatin haɗin kan ƙasa, wanda a motsinsa na 'yan kwanakin nan ya tabbatar da kalamansa.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin mambobin tsagin Adawa da zababben shugaban kasa ka iya naɗa wa a gwamnatinsa, ga su kamar haka:
1. Rabiu Musa Kwankwaso
Jagora kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, na ɗaya daga cikin waɗanda ake tsammanin zasu shiga majalisar Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya-bayan nan Kwankwaso ya tabbatar da rahoton cewa ya gana da shugaban ƙasa mai jiran gado a ƙasar Faransa, kuma ya nuna a shirye yake ya yi aiki da gwamnati mai zuwa.
2. Gwamna Nyesom Wike
Ɗaya daga cikin na sahun gaba da ba za'a yi mamaki ba idan ya shiga gwamnatin Tinubu duk da banbancin jam'iyya shi ne gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, mamban PDP.
A lokacin zaɓen 2023, ƙawancen Wike da Tinubu abu ne da ya fito fili kowa ya gani kuma zabaɓɓen shugaban kasan ya tabbatar da cewa gwamnan ya taimaka wa APC.
3. Ayo Fayose
Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma babban ƙusa a jam'iyyar PDP na cikin waɗanda ake tsammanin gani a sabuwar gwamnatin APC bayan ranar 29 ga watan Mayu.
Fayose bai ɓoye goyon bayansa ga Tinubu ba a lokacin zaɓe kuma ya bayyana dalilin da yasa suka lashi takobin yaƙar Atiku Abubakar, ɗan takara a inuwar PDP.
4. Chimaroke Nnamani
Nnamani, tsohon gwamna tsawon zango biyu a jihar Enugu kuma Sanatan Enugu ta gabas har sau biyu, ka iya shiga jerin yan majalisar Bola Tinubu bayan rantsarwa.
A lokacin kamfen babban zaɓen 2023, Nnamadi ya fito fili ya yi wa Bola Tinubu aiki wanda ta kai ga PDP ta kore shi daga cikin jam'iyyar. Daga baya ya sha kaye hannun LP a kokarinsa na komawa majalisa.
5. Reno Omokri
Tsohon hadimin shugaban ƙasa kuma mamban kamfen Atiku ya nuna gamsuwa da halaye da ɗabi'un zababben shugaban ƙasa.
Yayin martani ga kalaman Peter Obi cewa Yemi Osinbanji ya fi Tinubu cancanta da zama shugaban ƙasa, Omokri ya ce shugaba mai jiran gado ya fi Osinbajo da Obi kansa har sau 10.
6. Lamidi Apapa
Kwanan nan wasu suka fara zargin Tinubu ke ɗaukar nauyin shugaban tsagin jam'iyyar LP na ƙasa domin wani ɓangaren LP na masa kallon baragurbin kwai da ke neman kawo cikas a ƙarar da Obi ya kalubalanci nasarar Tinubu.
Duk da Mista Apapa ya musanta cewa Tinubu ke dafa masa yana duk abinda yake yi a LP, Amma ya ce a shirye yake ya amsa gayyatar zababɓen shugaban ƙasan.
Ganduje ya sallami kwamishinoni da hadimansa
A wani labarin na daban, Gwamna Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki Ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Gwamnan ya baiwa kwamishinoni, hadimai da sauran naɗe-naɗen siyasa wa'adin da zasu gama kwashe komatsansu su miƙa ragama hannun Sakatarori.
Asali: Legit.ng