Gwamna Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki

Gwamna Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki

  • Gwamna Ganduje ya rushe majalisar zartaswansa baki ɗaya yayin da ake tunkarar ranar rantsarwa 29 ga watan Mayu
  • Ya umarci kwamishinoni da hadimansa su miƙa ragamar ofishinsu hannun manyan Sakatarori ko daraktoci daga nan zuwa ranar Jumu'a
  • Nan da mako ɗaya zababben gwamnan Kano, Abba Ƙabir Yusuf, zai hau gadon mulki bayan nasarar da ya samu a zaben 2023

Kano - Gwamnan Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar zartarwa daga bakin aiki.

Premium Times ta rahoto cewa Ganduje ya rushe majalisar zartaswansa a wani ɓangare na shirye-shiryen miƙa mulki ga zababben gwamna ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Gwamna Ganduje.
Gwamna Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki Hoto: Abdullahi Ganduje
Asali: UGC

Babbar Sakatariya a ofishin Sakataren gwamnatin jihar Kano, Bilkisu Maimota, ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin 22 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Kara Rikita Jam'iyyar

Sanarwan ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yayin da wa'adin zango na biyu na mulkin gwamna Abdullahi Ganduje zai cika ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ya zama wajibi jami'an gwamnati da ke riƙe da kujerun siyasa su sauka daga mukamansu."
"Bisa haka ne, a hukumance muke umartan masu rike da naɗe-naɗen siyasa kama daga Kwamishinoni, mashawarta da sauran hadimai na musamman, mambobin gudanarwan hukumomi su miƙa ragamar ofisoshinsu."
"Dukkan waɗan da abun ya shafa ana umartan su miƙa ragama da duk wata kadarar gwamnati hannun Manyan Sakatarori ko Daraktoci daga nan zuwa ranar Jumu'a 26 ga watan Mayu."

Bugu da ƙari, Misis Bilkisu Maimota, ta ce wannan umarnin bai shafi masu rike da muƙaman da wa'adinsu bai ƙare ba kamar yadda kundin dokoki ya tanada.

Ta bayyana cewa Gwamna Ganduje ya gode tare da jinjinawa jami'an gwamnatin bisa gudummuwar da suka bayar iya karfinsu wajen kawo ci gaba ga jahar Kano.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Ganduje ya yi karin haske kan faifan muryarsa da ke yawo na sukar Tinubu

Mai girma Gwamna ya musu fatan Alheri a dukkan harkokin rayuwa da zasu sa gaba, inji Misis Maimota, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Tsohon Shugaban Jam'iyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

A wani labarin kuma Tsohon Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Kara Rikita Jam'iyyar ana dab da zaben gwamna a jihar Kogi.

Bayanai sun nuna gwamna Yahaya Bello, ya karbi tawagar masu sauya sheka daga PDP, lamarin da ake ganin babbar barazana ce ga burin Sanata Dilo Melaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262