Muhimmin Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Gana da Kwankwaso a Faransa, Jibrin
- Babba dalilin da ya jawo zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sa labule da Rabiu Kwankwaso a Faransa ya fito
- Honorabul Abdulmumini Jibrin, ya ce manyan 'yan siyasan biyu sun tattauna ne kan yadda za'a ƙara inganta haɗin kan ƙasa da kawo ci gaba
- Bayanai sun nuna cewa Jibrin ne ya shiga ya fita har ya haɗa zaman Tinubu da Kwankwaso saboda alaƙarsa da duka mutanen biyu
Zababben ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Abdulmumini Jibrin, ya yi ƙarin haske kan ganawar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da Rabiu Kwankwaso a Faransa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya gana da Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a zaben 2023 ranar Litinin 15 ga watan Mayu, 2023 a ƙasar Faransa.
A cewar Jibirin, shugaban ƙasa mai jiran gado ya zauna da Kwankwaso ne a kokrain ganin ya inganta haɗin kan ƙasa, fahimtar juna da kuma kawo ci gaba.
Meyasa manyan 'yan siyasan suka sa labule a Faransa?
Ɗan majalisar tarayyan ya ƙara da bayanin cewa a iya saninsa, Tinubu ba zai yi watsi da mutanen da suka taimake shi a lokacin babban zaben da ya gabata ba, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jibirin ya yi wannan ƙarin haske domin kawo karshen kace-nace kan lamarin a wani sakon murya da ya fitar ranar Lahadi, 21 ga watan Mayu, 2023.
Ɗan majalisar ya ce:
"Bana tunanin Tinubu zai yi watsi da waɗanda suka taimake shi lokacin zaɓe, amma yana da burin gina haɗin kan ƙasa, fahimtar juna da kawo ci gaba."
Haka nan kuma, kalaman Jibrin sun yi Alla-wadai da wani sautin murya, wanda aka ji gwamnnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna rashin jin daɗinsa da lamarin.
Shin Tinubu zai sasanta Ganduje da Kwankwaso?
Honorabul Jibrin ya yi bayanin cewa gabanin Tinubu ya sa labule da Kwankwaso, sai da ya tuntuɓi gwamna Ganduje na jihar Kano.
Ya ce Gwamna Ganduje da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa zasu iya sasanta duk wani saɓani da ya shiga tsakaninsu.
A wani labarin kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmai Ya Ja Hankalin Yan Najeriya Game da Sabuwar Gwamnatin Bola Tinubu da Zata Kama Aiki.
Alhaji Sa'ad Abubakar na III, ya ce shekaru 24 kenan da fara mulkin farar hula a Najeriya, ya kamata kowa ya jingine banbancin da ke tsakaninsa da yan uwansa yan ƙasa.
Asali: Legit.ng