Sarkin Musulmai Ya Fara Nema Wa Gwamnatin Tinubu Goyon Bayan Yan Najeriya

Sarkin Musulmai Ya Fara Nema Wa Gwamnatin Tinubu Goyon Bayan Yan Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya roki yan Najeriya su marawa gwamnatin Tinubu baya
  • Basaraken ya bukaci mutane su jingine duk wani abu da ya banbanta su, su haɗa kai wuri ɗaya domin ci da kasar nan gaba
  • Ya ce Najeriya na dab da kafa tarihin cika shekaru 24 da fara mulkin farar hula tun daga shekarar 1999

Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya roki yan Najeriya kan sabuwar gwamnatin da ake dab da rantsarwa.

Sultan ya roki baki ɗaya 'yan Najeriya su jingine banbance-banbancen addini, siyasa da al'adu, su haɗu wuri ɗaya su goyi bayan sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'a Abubakar III.
Sarkin Musulmai Ya Fara Nema Wa Gwamnatin Tinubu Goyon Bayan Yan Najeriya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sarkin ya yi wannan roko ne ranar Jumu'a a wurin kaddamar da kwamitin babban masallacin kasa (ANMMB) da kwamitin amintattu kan manufofin ilimi, lafiya da jin kai (MESH).

Kara karanta wannan

Dala $800m: Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Ƙara Sunkoto Bashi Bisa Sharadi 1 Rak

Ya ce lokaci ya yi da kowane ɗan Najeriya zai ba da gudummuwarsa a mulkin Demokuraɗiyya na ƙasar nan, wanda ya faro tun daga zuwan jamhuriya ta huɗu a 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Daily Trust, Sultan ya ce:

"Ƙasar mu da muke ƙauna na kan siraɗin sake kafa tarihi, nan da 'yan kwanaki ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za'a samu sauyin gwamnati daga mai ci zuwa wata. Shekaru 24 kenan muna mulkin farar hula."
"Damar da demokuraɗiyya ta baiwa mutane su yanke wanda suke son ya shugabance su abun sha'awa ne kuma ya zama wajibi mu guji wasa da ita. Mun ji daɗin tsawon lokacin da aka kwashe zuwa yanzu."

Bugu da ƙari, ya buƙaci 'yan Najeirya da su ba da duk gudummuwar da ya kamata wajen ganin an gudanar da bikin miƙa mulki lami lafiya ba tare da samun kowace irin matsala ba, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali

Nan da mako ɗaya da kwanaki 2, shugaba Muhammadu Buhari zai sauka daga kan madafun iko ya miƙa wa zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, wanda zai shafe shekaru 4.

Kaduna: Babban Abinda Ya Sa Ban Yi Shagalin Lashe Zaben Gwamna Ba, Uba Sani

A wani labarin kuma Zababben Gwamnan Kaduna ya bayyana ainihin dalilin da yasa bai shirya taron murnar samun nasara ba.

Malam Uba Sani ya ce akwai ayyukan al'umma a gabansa a matsayinsa na Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya zama dole ya maida hankali kan sauke nauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262