Ganawa Da Tinubu: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour, Apapa Ya Bada Sharaɗin Ganawa Da Zababben Shugaban Kasa

Ganawa Da Tinubu: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour, Apapa Ya Bada Sharaɗin Ganawa Da Zababben Shugaban Kasa

  • Shugaban tsagin jam’iyyar Labour Lamidi Apapa ya bayyana dalilin da ya sa zai amsa gayyatar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi masa
  • A cewar Apapa, dalilin da zai sa ya amsa gayyatar da Tinubu ya yi masa shi ne in ya sami izini daga shugabannin jam’iyya
  • Jam'iyyar ta Labour dai na fama da rikicin shugabanci, wanda ko a ranar Larabar sai da ɓangarorin da ke biyayya ga Apapa da Julius Abure suka fafata a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke Abuja

Abuja - Shugaban bangaren Labour Party (LP), Bashir Lamidi Apapa, ya bayyana da dalilin da zai sa ya amsa gayyatar tattaunawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Da yake magana a shirin safe na Arise TV a ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, Apapa ya ce zai amsa gayyatar da Tinubu ya yi masa, muddin shugabannin jam’iyyarsa suka amince, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

TInubu Apapa
Shugaban Tsagin Labour Party, Lamidi Apapa Ya Bada Sharaɗin Ganawa Da Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Lamidi Apapa
Asali: Facebook

Dalilin da ya sa zan amsa gayyatar Tinubu

Jaridar The Punch ta wallafa cewa, a yayin da yake amsa tambayoyi kan ko zai mutunta gayyatar da Tinubu ya yi masa na neman sulhu, Apapa ya ce zai yi hakan idan jam’iyyar ta amince.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Kafin na amsa gayyatar, zan tuntuɓi shugabannin zartarwa na jam’iyya ta, don haka idan suka ce in je, zan yi hakan. Idan shugabannin suka aminta, hakan ya zama matsayarmu kenan.”

Sannan kuma ya ce bayan amincewar jam'iyyarsa, Apapa ya ce akwai kuma buƙatar amincewar jam'iyyar APC da Tinubun ya ke ciki.

“Ba zai zama matsayata ba. Idan aka ce ku je, kun ga ya zama matsayar jam’iyya ba matsayar Alhaji Bashiru Lamidi Apapa ba.”
“Dukkanmu za mu je tare mu gan shi. Wato idan mun samu izini daga gidan da za mu je ganin nasa."

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa Ta 10: Ba A Yi Wa Yankin Arewa Adalci Ba a Tsarin Da Aka Zo Da Shi, Abdulaziz Yari

Ban karɓi N500m ba

A wani labarin da muka wallafa, shugaban tsagin jam'iyyar ta Labour Party Lamidi Apapa, ya ce bai karɓi N500m ba da zummar kawo cikas a shari'ar da ake yi tsakanin jam'iyyarsa da Tinubu.

Apapa ya yi kira ga ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar wato Peter Obi, kan ya sanya baki don sasanta rikicin shugabanci da ya addabi jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng