Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa na nuni da cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fara duba tsarin majalisar ministocinsa da kuma ta masu kula da tattalin arziƙi.

Za a rantsar da Tinubu ne dai a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.

Femi, Ganduje, Ribadu
Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi. Hoto: Punch, Premium Times
Asali: UGC

A rahoton wanda jaridar ta fitar ranar Laraba, 17 ga watan Mayu, ta bayyana cewa wata majiya ta shaida ma ta cewa, zaɓaɓɓen shugaban kasar na son mayar da hankali sosai wajen zaɓo mutanen da suka dace da za su taimaka masa wajen cimma duka manufofinsa.

Tinubu na son bai wa mara ɗa kunya

Majiyar ta bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya san cewa mutane sun sanya tsammani sosai a kan gwamnatinsa, kuma ya san irin gajen haƙurin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ban Gane Ba," Atiku Ya Maida Martani Kan Kiran da Sakataren Amurka Ya Yi Wa Tinubu Ta Wayar Tarho

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin haka ba ya so a samu matsala kan manufofin nasa, don haka nema yake son ya zamto ya gama zaɓar mutanen da za su yi aiki tare kafin 29 ga Mayu.

Kamar dai yadda majiyar wacce ba a bayyana sunanta ba ta bayyana, waɗannan su ne sunayen manyan ‘yan siyasar da ake tunanin Tinubu zai ba ministoci, da kuma ma'aikatun da za a tura su:

  1. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje (Kano) - Ministan harkokin noma da raya yankunan karkara
  2. Gwamna Nyesom Wike (Ribas) - Ministan harkokin cikin gida
  3. Dakta Kayode Fayemi - Ministan harkokin ƙasashen waje
  4. Farfesa Peter Okebukola - Ministan Ilimi
  5. Malam Nuhu Ribadu - Ministan harkokin 'yan sanda
  6. Sanata Aisha Binani - Ministar wutar lantarki
  7. Babatunde Ogala - Ministan shari'a
  8. Wale Edun - Ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsare
  9. M*ofo Boyo - Ministan mai
  10. Ayo Abina - Ƙaramin ministan tsare-tsare
  11. Femi Gbajabiamila - Shugaban ma'aikata
  12. Yewande Sadiku - Ministan masana'antu
  13. Farfesa Yemi Oke
  14. Iyin Aboyeji
  15. Dayo Israel
  16. Uju Ohanenye

Kara karanta wannan

“Shugabannin Ƙasa 120 Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu": Cewar Adamu Garba, Jigo a Jam'iyyar APC

Sai dai jaridar The Guardian ta wallafa cewa akwai wasu daga cikin ministocin gwamnatin Buhari da suka aika kokon bararsu zuwa ga Tinubu.

Ta ce wasunsu tun kan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Faransa suka rika aika masa da sakonni na neman a sanyasu cikin wadanda za a yi tafiyar da su.

Tanadin da Tinubu ya yi wa waɗanda ba za su samu muƙaman ministocin ba

Bugu da ƙari, majiyar ta bayyana cewa, akwai yiwuwar a sanya waɗanda ba su sami muƙamin ministan ba cikin hukumar masu kula da tattalin arziki.

Haka nan kuma, akwai yiwuwar a bai wasu daga cikinsu shugabantar wasu hukumomin da ke samar da kuɗaɗen shiga.

Akwai yiwuwar bai wa 'yan adawa muƙamai

A cewar majiyar, Tinubu na son bayar da muƙaman ministocin da sauran muhimman muƙamai ga 'yan jam'iyyar APC ne kawai.

Sai dai a shirye kuma ya ke ya yi bai wa wasu hazikai daga wajen jam’iyyar waɗanda ya ke ganin za su taimaka masa wajen cimma burinsa na farfado da tattalin arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng