Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana

Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana

  • An yi wa shugaban tsagin jam'iyyar Labour Party (LP), Lamidi Apapa, kwarmato a wajen kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ranar Laraba
  • Wasu daga cikin magoya bayan ɗayan tsagin jam'iyyar a wajen kotun, sun yi ta kiran 'Ole' (wata kalma mai nufin ɓarawo a Yarbanci), a yayin da ake ƙoƙarin fitar da Apapa daga cikin kotun
  • Wani mutum ya cire hular Apapa inda ya arce da ita, yayin da ake cigaba da yi masa kwarmato a wajen

Abuja - Wani mutum wanda ba a san kowane ne ba a ranar Laraba, 17 ga watan Mayun 2023, ya cirewa Lamidi Apapa, shugaban tsagin jam'iyyar Labour Party, hula sannan ya gudu da ita.

Mutumin dai ya cire hular Apapa ne lokacin da ya ke fitowa daga cikin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, bayan an saurari ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peter Obi, ya shigar kan zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Kuskure: An Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

An kunyata Lamidi Apapa a kotun zabe
Magoya bayan Labour Party sun kunyata Lamidi Apapa a kotu Hoto: Mrs Margaret Brownson Obi
Asali: Facebook

An yi ta kwarmato ana cewa 'Ole' (wacce ke nufin ɓarawo a Yarbanci) lokacin da Apapa ya ke ficewa daga kotun.

Apapa, wanda tunda ya farko ya tayar da hargitsi a cikin kotun, yana fita ne daga kotun lokacin da dandazon mutane suka baibaye shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na jam'iyyar Labour Party, wanda jami'an tsaro suka yi wa garkuwa, ya sha wuya wajen zuwa inda aka ajiye motarsa, yayin da mutanen suka yi ta bin sa.

Hatsaniyar ta ƙara yawaita ne lokacin da wani mutum daga cikin dandazon mutanen, ya cire masa hula, ya wurgar da ita a ƙasa, sannan ya ranta ana kare.

Rigima Ta Barke Tsakanin Tsagin Labour Party a Kotun Zabe

Da zu rahoto ya zo kan yadda hargitsi ya ɓarke a tsakanin tsagin jam'iyyar Labour Party (LP), a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, mai zamanta a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rigima Ta Barke Tsakanin Tsagin Jam'iyyar Labour Party a Kotun Zabe

Rigimar ta fara ne a tsakanin shugaban tsagin jam'iyyar, Lamidi Apapa, da babban darektan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Obi-Datti, Akin Osuntokun.

Jiga-jigan jam'iyyar sun yi musanyar kalamai masu kaushi, wanda har sai da ta kai an shiga tsakaninsu kafin ƙurar ta lafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng