Kakakin Majalisa Ta 10: Dalilin Da Yasa Na Goyi Bayan Abbas Maimakon Ɗan Jihata, Zulum

Kakakin Majalisa Ta 10: Dalilin Da Yasa Na Goyi Bayan Abbas Maimakon Ɗan Jihata, Zulum

  • Gwamnan Borno ya yi watsi da ɗan majalisar jiharsa, ya tabbatar da goyon bayansa ga Tajudden Abbas da Benjamin Kalu
  • Babagana Zulum ya ce mutanen Borno zasu so kakakin majalisar wakilai ya fito daga cikinsu, amma sun zabi haɗa kai da APC
  • Abbas da Kalu sun ziyarci gwamnonin arewa uku a ci gaba da yawon neman goyon baya gabanin rantsar da majalisa ta 10

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ce yana goyon bayan takarar Tajudeen Abbas a matsayin kakakin majalisar wakilai maimakon ɗan asalin jiharsa, Muktar Aliyu Betara.

Gwamna Zulum ya ce ya zaɓi ya jingine ɗan Borno, Betara, ya marawa Abbas baya saboda biyayya ga wanda jam'iyyar APC take goyon bayan ya ɗare kujerar a majalisa ta 10.

Babagana Zulum.
Kakakin Majalisa Ta 10: Dalilin Da Yasa Na Goyi Bayan Abbas Maimakon Ɗan Jihata, Zulum Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Idan baku manta ba jam'iyyar APC ta ɗauki Abbas daga jihar Kaduna da Benjamin Kalu daga jihar Abiya a matsayin waɗanda take goyon baya su zama kakaki da mataimakin kakakin majalisa.

Kara karanta wannan

‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa

Daily Trust ta rahoto cewa Betara ne mamba mai wakiltar mazaɓar Biu/Bayo/Shani a majalisar wakilan tarayya daga jihar Borno, Arewa maso Gabas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya shiga tawagar G-7, wacce fusatattun yan takarar kakakin majalisar suka kafa da nufin wargaza tsarin kason kujerun da jam'iyyar APC ta yi.

Wasu gwamnonin APC 5 daga Arewa ta Tsakiya, sun nuna rashin gamsuwarsu da kason APC, sun ce zasu zauna da Bola Tinubu.

Abinda ya sa zan goyi bayan Abbas - Zulum

Da yake jawabi sa'ilin ba Abbas da Kalu suka kai masa ziyara a Abuja, Gwamna Zulum ya ce:

"A madadin al'ummar jihar Borno, zamu yi farin ciki da alfahari idan muka samu mataimakin shugaban ƙasa da kakakin majalisa."
"Amma tunda zababben shugaban kasa ku yake so, idan Allah ya so ku ne zaku samu nasarar zama kakaki da mataimakin kakakin majalisa."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Wasu 'Yan Majalisa Sun Janye Daga Takarar Kakakin Majalisar Tarayya, Zasu Koma Bayan APC

Gwamnan ya roki 'yan takarar biyu su jawo sauran masu hangen kujerun a jiki domin haɗa kai tsakaninsu da kulla abota.

Daga nan, tawagar 'yan majalisun suka ziyarci gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da Simon Bako Lalong na jihar Filato.

Dagaske gwamna Inuwa ya baiwa ɗan takarar NNPP biliyan N2bn?

A wani labarin kuma Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fayyace gaskiya kan zargin ɗan takarar NNPP ya lamushe N2bn daga wurin gwamna Inuwa.

Honorabul Ayala ya ce labarin duk kanzon kurege ne da jam'iyyar APC ta kirkira da nufin ɓata wa Mailantarki suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262