Yadda Sanatoci Za Su Gujewa Kuskuren da APC Ta Tafka a 2015 – Shugaban Jam’iyya
- Godswill Akpabio ya dauki Sanatoci 40, sun ziyarci Shugabannin jam’iyya a Sakatariyar APC
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya gargadi ‘Yan majalisa kan maimaita kuskuren baya
- Jam’iyyar APC ta na goyon Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da Jibrin Barau (Kano) a zaben bana
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta fara kokarin ganin yadda wadanda ta ke so za su zama shugabannin majalisar tarayya ta goma da za a rantsar a bana.
Domin ganin abin da ya faru a 2015 bai maimaita kan sa ba, The Nation ta ce Abdullahi Adamu ya fadawa Sanatoci su tafi majalisa da wuri a ranar.
Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce za su cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ‘yan takaran jam’iyya su samu yin nasara.
Jawabin Sanata Abdullahi Adamu
"Ina so mu yi zabe ba tare da rikici ba, domin ko da kowa yana goyon bayan Akpabio, dokar majalisar kasa ta ce wajibi ne a shirya zabe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wadanda suke Sanatoci a cikinku kun san haka. Ba za mu bata tsari a ranar rantsar da shugaba ba.
Kilakin majalisa zai shirya zaben. Ina kuma fata za mu yi nasara. Amma ina jan-kunnenku, ka da a makara. An sha mu, mun warke yanzu."
- Abdullahi Adamu
Zababbun Sanatocin sun zauna da NWC
Adamu wanda yana majalisa a 2015 ya yi bayanin muhimmancin rike majalisa da yake zantawa da Akpabio da Sanatoci 40 da suka zauna da NWC a jiya.
Bayan wata kungiya ta ziyarci Sakatariyar APC a garin Abuja, Vanguard ta rahoto Abdullahi Adamu yana mai cewa bai dace a sake irin kuskuren 2015 ba.
Shugaban jam’iyyar yake cewa samun shugabannin majalisa ya na da muhimmanci, ya kuma ce kokarin da suke yi na dinke baraka yana haifar da ‘da mai ido.
Da wa aka yi zaman?
Gbenga Daniel, Ibrahim Geidam, Ipalibo Banigo, Olamilekan Adeola, Opeyemi Bamidele, Ali Ndume, Salihu Mustapha, da Mohammed Monguno sun je taron.
Haka zalika Tokunbo Abiru, Darlington Nwokocha, Asuquo Ekpenyong, Rufai Hanga, Idiat Adebule, Aziz Musa, Titus Zam, Neda Imazuen da kuma Shuab Salusi.
Rahoton ya ce an ga Yemi Adaramodu, Sadiku Ohere, Onyekachi Nwanba, Sarafadeen Ali, Yuniz Akintunde and Mutari Muhammad a sakatariyar jam’iyya mai-ci.
Tawagar ta hada da, Jim Kuta, Kenneth Eze, Ethan Williams, Emmanuel Demdi, Dakat Plang, Bola Ashiru, Jide Ipinsagba, Wasiu Esinlokun, da Howell Eyinsu.
Ragowar su ne Karimi Sunday, Cyril Fasuyi, Isa Jubrin, Nasiru Sani, Kaka Shehu Lawan, Ndubusi Patrick da Ibrahim Mohammed.
Meya faru a 2015?
Idan za a tuna a 2015, APC ta na goyon bayan Dr. Ahmed Lawan ya zama shugaban majalisar dattawa, amma Dr. Bukola Saraki ya mamayi jam’iyyarsa.
Kafin Sanatocin APC su hallara a majalisar dattawa bayan sun tafi taro, Dr. Bukola Saraki ya hada-kai da ‘yan PDP, shi da Ike Ekweremadu su ka ci zabe.
Asali: Legit.ng