Bai Kamata Ku Tsaya Binciken Gwamnatocin Baya Ba, Shawarin Umar-Radda Ga Zababbun Gwamnoni

Bai Kamata Ku Tsaya Binciken Gwamnatocin Baya Ba, Shawarin Umar-Radda Ga Zababbun Gwamnoni

  • Zababben gwamnan jihar Katsina Dikko Umar-Radda ya shawarci takwarorinsa da kada su tsaya binciken gwamnatocin baya
  • Umar-Radda ya yi wannan jawabi ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin 15 ga watan Mayu a Abuja
  • Ya kuma yi bayanin yadda zai kawo karshen rashin tsaro da cewa rashin adalci ne ya jawo hakan a bangarori da dama

Jihar Katsina - Zababben gwamnan jihar Katsina Dikko Umar-Radda ya shawarci takwarorinsa zababbun gwamnoni da kada su tsaya binciken gwamnatocin baya da zaran sun karbi mulki.

Umar-Radda ya ce zababbun gwamnonin ya kamata su mai da hankali wurin tabbatar da zaban wadanda suka kware a bangarori da dama ba tare da bambancin jam’iyya ba.

Umar-Radda ya shawarci zababbun gwamnoni
Bai Kamata Ku Tsaya Binciken Gwamnatocin Baya Ba, Shawarin Umar-Radda Ga Zababbun Gwamnoni, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Zababben gwamnan ya yi wannan bayani ne lokacin da yake hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin 15 ga watan Mayu a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan kana so ka yi nasara a matsayin ka na gwamna ko wani mukami da kake da shi dole ka zabo mutane kwararru ta bangarori da dama don kawo ci gaba.
“Bai kamata zababbun gwamnoni su tsaya binciken meye gwamnati ta aikata ba, ya kamata su fara aiki kawai ba tare da bata lokaci ba, su ja layi kawai, daga nan sai su samar da shugabancin da ya kamata ga jiharsu.”

Ya ce gwamnatinsa za ta fi maida hankali akan matsalolin tsaro dake addabar yankunansu, inda ya yi alkawarin ya shirya tsab don kawo karshen wannan matsalar tun daga tushe.

Umar-Radda ya ce tushen rashin tsaro, rashin adalci ne wa Fulani ya jawo

Ya bayyana tushen matsalar tsaron da cewa rashin adalci ne da ake yiwa Fulani tun da jimawa, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni

Ya kara da cewa:

“Kowa yasan irin yadda abubuwan nan suka fara, rashin adalci ne da ake yiwa Fulani tun a can baya, kuma gwamnati bata dauki mataki akai ba, idan kaje kauyuka za ka ga basu da makaranti da asibitoci ko ruwan sha, ba su moran komai daga gwamnatoci."

Rashin Tsaro: Za Mu Saka Matasa Su Yaki Yan Bindiga a Katsina - Umar-Radda

A wani labarin, dan takarar gwamnan jihar Katsina, Umar-Radda ya ce zai yi amfani matasan jihar in har ya zama gwaman don yakar 'yan bindiga.

Umar-Radda ya bayyana haka yayin da yake ganawa da jama'a da sukayi dafifi a yakin neman zabensa a karamar hukumar Batsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.