“Shugabannin Ƙasa 120 Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu": Cewar Adamu Garba, Jigo a Jam'iyyar APC
- Ana ta ci-gaba da tafka muhawara kan bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu
- Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki ya ce za a miƙawa Tinubu mulki kamar yadda aka tsara kuma babu abinda zai hana faruwar hakan
- Tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba ya ci-gaba da cewa a yanzu haka shugabannin ƙasashe 120 ne suka nuna sha’awar halartar bikin rantsar da Tinubu
Abuja - Tsohon dan takarar shugabancin ƙasa kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Adamu Garba, ya bayyana dalilin da ya sa ba za a iya dakatar da bikin miƙawa Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu ba.
Garba ya bayyana cewa sama da shugabannin kasashe 120 ne suka nuna sha’awarsu ta halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
"Mahmud Yakubu Tsohon Yaro Na Ne," Pater Obi Ya Fallasa Maganar da Ya Faɗa Wa Shugaban INEC Gabanin Zaben 2023
Adamu ya kuma ce bikin da za a gudana a ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023, ya na nan za a yi babu fashi.
Masu shigar da ƙara akan Tinubu wasa suke yi
Adamu ya ƙara da cewa masu ƙoƙarin ganin an dakatar da ƙaddamar da Tinubu wasa kawai suke yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata hira da aka yi da shi a Arise TV ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, jigon na APC ya bayyana cewa waɗanda suka shigar da ƙara don dakatar da bikin rantsar da Tinubu wasa suke yi.
A cewarsa:
“A ranar 29 ga Mayu, 2023 za a yi bikin rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban tarayyar Najeriya da kuma Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban tarayyar Najeriya.”
Kuna bata lokacinku, kotu ba za ta hana rantsar da Tinubu ba, Adamu ga 'yan adawa
Ya kuma bayyana cewa babu wani umarni da kotu za ta bayar na hana rantsar da shugaban ƙasar. Ya ce masu shigar da ƙarar ma kawai suna ɓata lokacinsu ne.
Ya ce dalili kuwa shine zaɓe ya gudana lami lafiya ta hanyar amfani da na'urori kuma an gudanar da shi a idon duniya.
Duk duniya za ta haɗu a Najeriya
Adamu ya ƙara da cewa:
“Ina gaya muku a yanzu haka, akwai shugabannin ƙasashe 120 da suka nuna sha’awar zuwa bikin naɗin shugaban ƙasa mai jiran gado da mataimakinsa, to me kuma zamu kira wannan.
“Wasu mutane ne kawai suka fito daga uwa duniya suna cike wasu takardu a kotu da zummar wai su hana bikin da ya shafi duniya gaba ɗaya, menene wannan in ba abin dariya ba.
"Kamar yadda na ke gaya muku, duk duniya ce za ta taru a Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu don nuna goyon baya ga dimokuraɗiyyar Najeriya."
Ga hirar a kasa:
Kotu ta bijiro da sabbin batutuwa ga masu son hana rantsar da Tinubu
A wani labarin da muka wallafa a baya, wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta nemi mazauna Abuja da suka shigar da kararsu kan Tinubu da su zo su yi mata bayani.
Mutanen dai sun shigar da kara ne inda suke neman kotu ta haramtawa alkalin alkalai damar rantsar da zababben shugaban kasar.
Asali: Legit.ng