Kotun Zabe: Atiku da Namadi Sambo Sun Nemi Mambobin PDP Su Cure Wuri 1
- Atiku Abubakar da Namadi Sambo sun nuna alamun sa rai da nasara a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa
- Atiku ya nemi mambobin PDP su cure wuri ɗaya kana su tsammaci samun nasara a karar dake gaban Kotu
- Namadi Sambo ya koka da yadda ake kara samun rikici-rikice tsakanin 'ya'yan PDP musamman a matakin jihohi
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a babban zaben 2023, Atiku Abubakar, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ba su cire rai da samun nasara a Kotu ba.
Atiku da Namadi Sambo sun roki mambobin jam'iyyar PDP su dunƙule wuri guda kuma karsu cire rai da samun nasarar jam'iyyar a Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa.
Jiga-jigan biyu sun faɗi haka ne a wurin liyafar da ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya wa zababbu, masu ci, da gwamnonin PDP masu barin gado a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.
A nasa jawabin, Atiku Abubakar, ya buƙaci shugabannin jam'iyyar PDP su sake nazari kana su lalubo wasu dabaru waɗanda zasu taimakawa jam'iyyar ta sake mamaye siyasar ƙasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Namadi Sambo ya koka kan rikicin cikin gida
Haka nan a ɓangarensa, Sambo ya nuna damuwarsa kan yawan a kora da dakatar da mambobin PDP, wanda ke cin kasuwa a jihohin Najeriya, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Bisa haka, Namadi Sambo ya yi kira ga muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa ya gaggauta shiga lamarin kuma ya bi duk matakan da ya kamata a cikin gida a sulhunta komai.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a wurin wannan liyafa kaɗai, wacce jiga-jigan suka yi wannan magana, ya isa tabbatar da halin rigingimun da PDP ke ciki.
Gwamnonin G-5 karkashin gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ba su je wurin ba duk da an yi tsammanin ganisu a wurin, lamarin da ya kawo cikas a yunkurin fara neman sulhu, Daily Trust ta rahoto.
Majalisa Ta 10: Tinubu Ba Zai Maimaita Kuskuren da Buhari da Jonathan Ba, Shettima
A wani labarin kuma Mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, Kashim Shettima, Ya ce Tinubu ba zai yarda ya yi kuskuren Buhari da Jonathan ba.
Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ya ce matsalar da Buhari ya samu da majalisar wakilai na ɗaya daga cikin naƙasun da gwamnatinsa ta samu.
Asali: Legit.ng