Shugabancin Majalisar Dattawa: Yari, Kalu da Musa Sun Kai Kokensu Wurin Adamu
- Abdulaziz Yari, Orji Uzor Kalu da Sanata Mohammed Musa, sun ziyarci shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Adamu domin kai kokensu kan batun shugabancin majalisa
- Sun ce ba su yarda da tsarin da jam'iyyar APC ta yi na iyakance kujerar ga wani yanki kaɗai, maimakon bai wa kowa dama
- Abdullahi Adamu ya ce za su yi zama da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar
Abuja - Mai tsawatarwa a majalisar dattawa Orji Uzor Kalu, Abdulaziz Yari zaɓaɓɓen Sanata daga Zamfara, da kuma Mohammed Musa daga Neja, sun kai kokensu na nuna ƙin amincewarsu da zaɓin da APC ta yi na wanda zai shugabanci majalisar.
Jam'iyyar ta dai zaɓi tsohon ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio da kuma Barau Jibrin, daga Kano a matsayin shugaban majalisar ta dattawa da mataimaki, The Cable ta rahoto.
Ba mu gamsu da tsarin da aka yi ba
Abdulaziz Yari ya shaidawa shugaban jam'iyyar, Abdullahi Adamu a jiya Alhamis cewa basu gamsu da wannan tsari da aka yi ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yari bayan miƙa takardar koken nasu ya ce:
“Mun zo nan ne domin mu gabatar da takardar kokenmu gareka, sannan kuma mu shaidawa wannan gida mai albarka cewa ba mu gamsu da tsare-tsaren da aka yi ba.”
“Abinda muke tsammani daga gareku shine ku ba kowa dama ya nema, ba wai ku iyakance cewa 'yan wani yanki ne kawai za su iya neman kujerar ba.”
A nasa ɓangaren, Abdullahi Adamu ya ce shubancin jam'iyyar zai duba takardar koken nasu domin yi musu abinda ya dace.
Ba mu gama yanke hukunci ba tukun
Ya ƙara da cewar har yanzu ba su gama yanke hukunci ba, a saboda haka ya ɓuƙaci da su dakata da ƙorafe-korafen. Sannan kuma ya bayyana cewa ra'ayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Tinubu ya na da matuƙar tasiri akan batun.
Adamu ya ƙara da cewa dole ne su bai wa shugaban haɗin kai daidai gwargwado, kuma idan ya dawo ƙasar daga tafiyar da ya yi, za a zauna domin cimma matsaya.
Adamu yace:
“Bazan iya cewa komai ba a yanzu, zan jira har zuwa lokacin da za mu yi zama da sabon shugaban ƙasar.”
Bai kamata a ware shugabancin ga wani yanki ba kadai
Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisa suka tuntuɓi Adamu don yi masa ƙorafi kan batun tsarin tura kujerar wa wani yanki guda ɗaya.
Sanata Kalu da ya ke nasa jawabin ya ce bai kamata jam'iyyar APC ta yanke hukuncin ware shugabancin majalisar ga wani yanki kadai don duba da yawan kuri'un da suka bayar ko kuma don wani abu ba daban.
Channels TV ta samu cewa daga cikin waɗanda suka halarci zaman baya ga shugaban jam'iyyar wato Abdullahi Adamu, akwai Sakataren APC na ƙasa, Iyiola Omisore tare da shugabar mata ta jam'iyyar ta APC, Dakta Beta Edu.
Yari da Wasu Fusatattun Sanatoci 3 Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Yi Kus-Kus da Shugabannin APC
A labarinmu na baya, mun bayyana muku cewa zababben shugaban kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wadanda ya ke su su jagoranci majalisar ta dattawa.
Tinubu ya dai zabi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio ya shugabanci majalisar, da kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin a matsayin mataimaki.
Asali: Legit.ng