Ana Dab Da Ya Bar Ofis, Gwamnan Jihar Taraba, Ya Fitar Da N2bn Domin Siyo Motocin Kece Raini
- Gwamnan jihar Taraba ya amince a fitar da N2bn domin a siya masa motocin kece raini da shi da mataimakinsa
- Bayan mataimakinsa, har da matansu za a gwangwaje da sabbin motoci na gani na faɗa domin amfanin su
- A cikin kuɗin gwamnan da matarsa za su samu N1.3bn, sannan mataimakinsa da matarsa za su samu N750m
Jihar Taraba - Ana saura ƙasa da kwana 18 wa'adin mulkinsa ya ƙare, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya amince da fitar da N2bn, domin siyo motocin kece raini ga kansa, mataimakinsa da matansu.
Wani majiya a wajen taron da aka amince a fitar da kuɗin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya gayawa Premium Times cewa, an amince da fitar da kuɗin ne a lokacin zaman majalisar zartaswar jihar, wanda Ishaku ya jagoranta.
"Gwamna Darius Ishaku a lokacin zaman mu na majalisar zartaswa, ya nemi ƴan majalisar da su amince da takardar da ya gabatar domin siyo motoci ga karan kansa, mataimakinsa da matansu. Kuma cikin gaggawa aka amince da hakan ba tare da wata jayayya ba." A cewarsa
Ya bayyana cewa majilisar tace tun lokacin da gwamnan ya hau mulki a shekarar 2019, da shi da mataimakinsa suna amfani ne da tsaffin motocin da suka gada a wajen gwamnatin da ta gabace su, saboda haka sun cancanci jihar ta siya mu su sabbin motoci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda kasafin kuɗin zai kasance
Majiyar ya kuma yi bayanin cewa, a takardar da gwamnan ya gabatar, da shi da matarsa za su samu sama da N1.3bn, sannan mataimakinsa da matarsa za su samu N750m domin siyan motocin.
Majiyar ya kuma cigaba da cewa a ƙarƙashin wannan yarjejeniyar, gwamnan zai samu motoci guda biyu ƙirar Toyota Land Cruiser SUV, motocin rakiya guda biyu ƙirar Toyota Hilux da safayar mota ɗaya. Sannan matarsa za ta samu mota ƙirar Land Cruiser SUB da motar rakiya guda ɗaya.
Haka kuma, mataimakin gwamnan, Haruna Manu, zai samu motoci biyu ƙirar, Land Cruiser SUV da motar rakiya guda ɗaya, sannan matarsa za ta samu mota guda ɗaya ƙirar SUV, da safayar mota ɗaya.
Abinda kwamishiniyar watsa labaran jihar tace
Ko da aka tuntuɓi kwamishinar watsa labaran jihar, Lois Emmanuel, ba ta tabbatar ko musanta aukuwar hakan ba, cewar rahoton Tracknews.
"Bana cikin jihar nan. Ban da masaniya kan hakan amma zan tabbatar." A cewarta
Sai dai, an hango ta a wajen ƙaddamar da wasu gidaje da gwamnan jihar, ya yi a Jalingo, babban birnin jihar.
Gwamnati Ta Dauki Nauyin Maniyyatan Kiristoci 300 Zuwa Isra’ila Da Jordan Don Sauke Farali A Enugu
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Enugu ta ɗauki nauyin wasu masu sauke farali na addinin Kirista zuwa ƙasar Isra'ila da Jordan.
Gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi, shine yas tabbatar da hakan, inda ya ce sun ɗauki nauyin mutum ɗari uku.
Asali: Legit.ng