Wase Da Yan Takarar Shugabancin Majalisa 5 Sun Gana da APC NWC
- Mataimakin kakakin majalisar tarayya ta 9, Idris Wase, ya ziyarci Sanata Abdullahi Adamu da wasu mambobin NWC
- Jam'iyyar APC ta ce Wase tare da rakiyar wasu mambobin majalisar wakilai sun gana da shugabannin jam'iyya yau Laraba
- Hakan ya biyo bayan matakin APC na goyon bayan Tajudeen Abbas a matsayin ɗan takarar kakakin majalisa na maslaha
Abuja - Mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Idris Wase, ya jagoranci tawagar 'yan takarar kujerar kakakin majalisa 5 sun gana da mambobin kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC).
The Nation ta tattaro cewa wannan taro na fitattun yan majalisa da shugabannin APC na ƙasa ya zo ne yayin da yawon kama kafa da neman shawari ke cin kasuwa a jam'iyya mai mulki.
Mambobin majalisar wakilai da suka halarci zaman sun haɗa da Honorabul Sani Jaji daga Zamfara, Honorabul Yusuf Gagdi daga Filato da Honorabul Muktar Betara daga jihar Borno.
Sauran sun kunshi, Honorabul Mariam Onuuaha daga jihar Imo; Honorabul Sada Soli daga Katsina, Honorabul Femi Bamishile daga Ekiti, Honorabul Abubakar Hassan Nakraba daga Nassrawa da kuma Honorabul Ahmed Jaha daga Borno.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan gana wa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan jam'iyyar APC ta fitar da 'yan takarar da take goyon baya a kujerun shugabancin majalisar tarayya ta 10.
Jam'iyyar APC ta tabbatar
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita, jam'iyyar APC mai mulki ta tabbatar da ganawar Adamu, mambobin NWC da yan takarar kujerar kakakin majalisa.
Jam'iyyar APC ta ce:
"A ci gaba da yawon neman shawari game da shugabancin majalisar tarayya ta 10, mataimakin kakakin majalisar wakilai ta 9, Honorabul Idris Wase tare da rakiyar yan majalisa sun ziyarci Abdullahi Adamu da wasu mambobin NWC."
Bola Tinubu Ya Tafi Nahiyar Turai Kwanaki 19 Gabanin Rantsarwa
A wani labarin kuma Zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shilla nahiyar Turai domin tasa muhimman abu guda 2
Mai magana da yawun Tinubu, Mista Tunde Rahman, ya ce shugaba mai jiran gado da tawagarsa sun bar filin jirgin Abuja da tsakar ranar Laraba 10 ga watan Mayu.
A cewarsa, Tinubu ya zabi tafiya turai ne domin guje wa yan kamun kafa da ka iya damunsa yayin da ake tunkarar ranar rantsarwa.
Asali: Legit.ng