Ana Saura Kiris Ya Bar Ofis, Gwamnan APC Ya Nada Sabbin Kwamishinoni
- Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya yi naɗin wasu sabbin kwamishinoni a gwamnatinsa mai barin gado kwanan nan
- Umahi ya naɗa kwamishinonin ne, yayin da ya rage saura kwanaki 20 ya yi bankwana da kujerar gwamnan jihar
- Gwamnan ya buƙaci sabbin kwamishinonin da su yi aiki tuƙuru a cikin ƴan kwanakin da suka rage domin cigaban jihar
Jihar Ebonyi - David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya rantsar da sabbin kwamishinoni huɗu a gwamnatinsa ana saura kwana 20 ya bar ofis.
A cewar rahoton The Cable, an rantsar da kwamishinonin ne ranar Talata, fadar gwamnatin jihar da ke a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Kwamishinonin sun haɗa da Enekwachi Akpa, tsohon mai ba gwamnan shawara ta musamman kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Obianuju Aloh, tsohon SSA na gwamnnan kan sufurin jiragen sama da fasaha.
Sauran sun haɗa da, Emeka Nwode, tsohon SSA na gwamnan kan harkokin shari'a da Uchenna Nwankpuma, tsohon SSA na gwamnan kan aikace-aikace na musamman.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya shawarci kwamishinonim da su yi amfani da damar da su ke da ita, wajen ganin sun bar tarihi mai kyau wajen hidimtawa jihar da al'ummar ta, cewar rahoton Gazettengr.
Umahi ya kuma tarbi sabbin ma'aikata 400 da aka ɗauka domin tashar filin tashi da sauka ta ƙasa da ƙasa ta Muhammadu Buhari, a Onueke, cikin jihar Ebonyi.
Ya roƙe su da su nuna jajircewa da kishi wajen gudanar da ayyukansu, inda ya ce tashar jirgin saman, na ɗaya daga cikin ayyukan da jihar ke taƙama da su.
Tsohon Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Kashin Da Ya Sha a Kotu, Ya Ba Gwamnan PDP Shawara
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda tsohon gwamnan APC na jihar Osun ya saduda ya fawwalawa Allah komai bayan ya sha kashi a kotun ƙoli, a hannun gwamnan PDP.
Gboyega Oyetola ya taya gwamna Ademola Adeleke, murnar nasarar da ya yi a kansa, inda ya buƙace shi da mayar da hankali wajen ciyar da jihar gaba.
Oyetola ya kuma ce ya amince da hukuncin da kotun ƙolin ta yanke kan ƙarar da ya shigar a gabanta.
Asali: Legit.ng