Sabon Sanata Zai Birkita Lissafi Ya Fado Cikin Takarar Shugaban Majalisar Dattawa
- Patrick Ndubueze ya sanar da shugabannin jam’iyyar APC zai nemi shugaban majalisar dattawa
- Zababben Sanatan na jihar Imo ta Arewa ya taba zama ‘dan majalisar wakilan tarayya tun a 1992
- Wannan karo Ndubueze yana neman goyon bayan NWC da Sanatoci domin ya shugabanci majalisa
Abuja - Zababben Sanata da zai wakilci yankin Arewacin jihar Imo, Patrick Ndubueze ya ayyana burinsa na neman takarar shugaban majalisar dattawa.
Patrick Ndubueze ya sanar da jam’iyyarsa ta APC hakan a wata wasika da ya aikawa majalisar gudanarwa ta kasa, Premium Times ta fitar da rahoton.
Kafin ya lashe zaben Sanata a 2023, ‘dan siyasar ya taba wakiltar mazabarsa ta Okigwe a majalisar wakilan tarayya a 1992, shekaru fiye da 30 da suka wuce.
Rahoton ya ce yanzu akwai mutane uku daga Kudu maso gabas da suke hangen shugabancin majalisar, akwai Osita Izunaso da Sanata Orji Uzor Kalu.
Jihar Imo ta samu 'yan takara 2
Ndubueze yana kishiyantar takarar Osita Izunaso daga Imo da kuma shugaban masu tsawatarwa bayan Dave Umahi daga jihar Ebonyi ya janye takararsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wasikar da ya aikawa NWC, Leadership ta ce zababben Sanatan ya ce lokaci ya yi da za a samu natsattsen shugaba mai tunani da taimakon al’umma.
Hon. Ndubueze ya cancanta
Hon. Ndubueze yana ganin ya cancanci ya jagoranci Sanatocin Najeriya a majalisa ta goma.
Abin da ya ke tinkaho da shi, shi ne ya taba zama ‘dan majalisa, sannan ya fi shekaru 35 yana siyasa kuma har gobe ana yi masa kallon mutum mai kima.
‘Dan siyasar ya roki shugabannin APC na kasa su mara masa baya domin ya cin ma wannan buri.
Baya ga haka, Ndubueze ya rubuta wasika zuwa ga wadanda za su zama abokan aikinsa a zauren majalisa, ya na rokon su ba shi kuri’arsu a zaben bana.
Wasikar ta hada da roko ga zababbun ‘yan majalisar dama su zauna da shi domin ya yi masu magana ido da ido, watakila hakan ya taimakawa takararsa.
Tikitin Taju/Kalu a Majalisa
An ji labari cewa an ware kujerar shugaban majalisar wakilai zuwa jihar Kaduna kuma Abbas Tajuddeen mai wakiltar mazabar Zariya ne wanda aka dauka.
Haka zalika wani jigo a APC ya nuna jam’iyya da zababben shugaban kasa sun gamsu kujerar mataimakin shugaban majalisa ta tafi yankin Kudu maso gabas.
Asali: Legit.ng