Majalisa Ta 10: Tinubu Ya Ayyana Wadanda Yake So, Yari Ya Ce Zababben Shugaban Kasar Ya Yi Kadan
- Abdul’Aziz Yari ba zai janye takarar da yake ni na shugabancin majalisar dattawa a 2023 ba
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya nuna Bola Tinubu bai isa ya tsaida wa sanatoci shugabansu ba
- Akwai yiwuwar Yari ya gwabza da Godswill Akpabio wanda ake tunanin jam’iyya tana goyon baya
Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Zamfara kuma zababben Sanata, Abdul’Aziz Yari bai da niyyar hakura da neman takarar shugabancin majalisa.
A ranar Lahadi, Daily Trust ta fitar da labari cewa Alhaji Abdul’Aziz Yari ya nuna babu wani abin da zai sa ya fasa harin kujerar majalisar dattawa.
A daidai lokacin da wasu da suka yi sha’awar wannan mukami su ka hakura, zababben Sanatan Yammacin Zamfara ya nuna ba zai ki takara ba.
Tuni Dave Umahi wanda zai wakilci Ebonyi ta Kudu da Sanata Muhammad Ali Ndume na Borno ta Kudu su ka janyewa Sanata Godswill Akpabio.
Abdul’Aziz Yari yana kan bakarsa
A bangarensa, an rahoto Yari yana cewa goyon bayan da Godswill Akpabio ya samu daga Bola Tinubu ba zai hana shi shiga takarar majalisar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya bayyana haka ne yayin da ya zauna da ‘yan kuniyar Tinubu/Shettima Network (TSN) a karkashin jagorancin Kailani Muhammad.
TSN ta hadu zababben Sanata
Kungiyar Tinubu/Shettima Network ta na cikin masu goyon bayan tsohon Gwamnan, saboda haka suka yi wani zama da shi ranar Asabar a garin Abuja.
Tsohon shugaban kungiyar gwamnonin kasar ya ce sha’anin shugabancin majalisa yana cikin kundin tsarin mulki, ba umarnin wani ake karba ba.
A cewar Yari, Sanatoci ne suke da hakkin su zabi wanda suke so ya jagorance su a majalisar dattawa, ba wani daga waje ne zai tsoma masu baki ba.
Godswill Akpabio/Barau Jibrin da Taju/Ben Kalu
Rahotanni sun nuna Godswill Akpabio/Barau Jibrin ne wanda zababben shugaban kasa yake goyon bayan su rike shugabancin majalisar dattawa.
A majalisar wakilan tarayya kuwa, Tinubu ya gamsu da Abbas Tajuddeen (Kaduna) da Benjamin Kalu (Abia) a matsayin shugaba da mataimakinsa.
Gwarazan Majalisa ta 9
Ku na da labari yayin da Femi Gbajabiamila ya jagoranci majalisar wakilai, akwai wasu 'yan majalisa da suka yi zarra a bakin aiki daga 2019 zuwa yau.
Haka zalika a karkashin jagorancin Ahmad Lawan, an samu Sanatoci irinsu Uba Sani da suka yi fice wajen kawo kudirori a zauren majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng