Kalu, Umahi ko Akpabio: Ganduje Ya Fadi Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya

Kalu, Umahi ko Akpabio: Ganduje Ya Fadi Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya

  • Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana wanda zai kasance shugaban majalisar dattawa ta 10.
  • Ganduje ya bayyana tsohon ministan Naija Delta, Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji kujerar majalisar
  • Gwamnan ya yi wannan bayanin ne bayan kammala ganawa da gwamnan jihar Kuros Ribas, Ben Ayade ranar Alhamis 4 ga watan Mayu.

Jihar Kuros Riba - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bada haske game da wanda zai zama shugaban majalisar dattawar Najeriya zubi ta 10.

Gwamnan ya ce tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa.

ganduje, akpabio
Ganduje, Umahi, Kalu, Akpabio, Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Ganduje ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu a lokacin da ya ke ganawa da gwamnan jihar Kuros Riba a Calabar babban birnin jihar.

Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan Shugaba Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganduje ya fadi wanda zai zama shugaban majalisa

Ganduje ya kara da cewa an riga an zabi Akpabio a matsayin shugaban amma bai yi bayanin cewa ko wannan hukunci na shugabannin jam’iyyar APC mai mulki ne ko sabanin haka ba.

"Shugaban majalisar dattawa na Najeriya zai zo ne daga Kudu maso Kudu, kuma wannan ba kowa ba ne illa tsohon gwamnan Akwa Ibom, in ji shi.

Sanatocin APC 2 Suna Rububi a Kan Kuri’un ‘Yan PDP a Majalisar Dattawa ta 10

A wani labarin, a kokarin ganin sun yi nasaran samun shugabancin majalisa, Abdulaziz Yari (Zamfara) da Godswill Akpabio (Akwa Ibom) suna kokarin ganin sun gana da 'yan adawa don samun goyon bayan kujerar shugabancin majalisa.

Rahotanni sun tattaro cewa Godswill Akpabio da Abdulaziz Yari su na kokarin ganin yadda za su samu samu kuri’un Sanatocin PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje Ya Fadi Sanatan da Zai Gaji Lawan, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisa

Hakan ba wani bakon abu ba ne a tarihin siyasar Najeriya, an dade ana ganin 'yan siyasa da neman goyon bayan 'yan jam'iyyun adawa, musamman tun bayan dawowar dimokradiya a wannan kasa,

Zababbun sanatocin biyu na daga cikin wadanda jam'iyya mai mulki ta APC nan ba da dadewa ba, in dai ba a manta ba a watan Afrilu na wannan shekara ne aka gudanar da babban zabe da yazo da wasu al'amura da ba a saba gani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.