Abba Gida-Gida Ko Gawuna: Allah Ne Kadai Ya San Wa Zan Mika Wa Mulkin Kano, Ganduje
- Gwamnan Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce Allah ne kadai yasan wa zai mikawa mulki a karshen wannan wata da muke ciki
- Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin kaddamar da sabbin hanyoyi da gwamnatinsa ta aiwatar, a jihar cikin ‘yan shekarun nan
- Gwamnatin APC dai ta maka Hukumar Zabe da kuma jam’iyyar NNPP a kotu bisa zargin magudin zabe da ya bai wa Abba Kabir Yusuf nasara.
Jihar Kano - Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Allah ne kadai yasan wanda zai mika wa ragamar mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara.
Gwamna ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke kaddamar da sabbin hanyoyi a jihar.
Idan ba a mantaba jam’iyya mai ci ta APC a jihar ta maka Hukumar Zabe da kuma jam’iyyar NNPP a kotu bisa zargin tafka magudi lokacin zaben gwamnan jihar ya gabata a watan Maris na wannan shekara, jaridar Daily Trust ya tattaro.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ganduje ya kafa kwamiti
A watan Afrilu da ta gabata ne gwamna Ganduje ya kafa kwamitin mutum 17 daga ma’aikatu da dama don mika mulki ga sabon zababben gwamnan jihar.
Sannan kwamitin na da karin mamabobi 100 don taimaka musu wurin mika mulki cikin aminci ba tare da wata matsala ba, kamar yadda IReporter ta tattaro.
Me gwamna Ganduje ya ce
Yayin kaddamar da sabbin titunan, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce:
“Daidai ne gwamnati ta gaji ayyuka, muma mun gaji ayyuka a gwamnatin baya kuma mun karisa su.
“Muma kuma zamu bar wasu ayyuka ga gwamnati mai zuwa, tabbas Allah ne kadai yasan wa zan mika wa mulki a karshen watan nan, ta yiyu APC ko NNPP."
Sarautar Kano: Na Kirkiri Masarautun Kano Ne Don Su Zauna Daram, Ganduje Ga Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya kirkiri masarautun Kano ne badan wani yazo ya rusa su ba.
Ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake jawabi a bikin ranar ma’aikata a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano, inda yace Allah ba zai bari wani ya tarwatsa su ba.
Gwamnan a baya ya rarraba masarautun ne kashi biyar, in da ya tsige Muhammadu Sunusu II daga mulki.
Asali: Legit.ng