Jam'iyyar NNPP Ta Kori Duka Shuwagabanninta Na Jihohin Ogun Da Delta, Ta Bayyana Dalili
- NNPP ta sanar da rushe shugabancin jam'iyyar a duka matakai a jihohin Delta da Ogun
- Ta zargi shuwagabanni da mambobinta na jihohin da haɗa kai da wata jam'iyya gami da amsar kuɗaɗe
- Jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar Agbo Major ya ƙara da cewa babu wata jam'iyya da zata lamunci irin hakan
Abuja - Ofishin shugabancin jam'iyyar NNPP na ƙasa ya sanar da korar duka shuwagabannin jam'iyyar na jihar Delta da Ogun bisa ayyuka na cin amana da jam'iyyar ta ke zargin sun yi ma ta a babban zaɓen da ya gabata. Jam'iyyar ta ce shuwagabannin na ta na waɗannan jihohi sun saɓa da tsarin jam'iyyar inda su ka goyi bayan wasu 'yan takarkarin.
Jami'in hulɗa da jama'a na ƙasa na jam'iyar ta NNPP Dakta Agbo Major ne ya sanar da hakan a yayin da ya ke hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja. Ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar na jihar Ogun kwamared Olaposi Sunday Ogini da kuma shugaban jam'iyyar na jihar Delta Chief Efe Tobor sun tafka manyan laifuka ga jam'iyyar a zaɓen da ya gabata.
Lauyoyi 50 Za Su Kare Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasa Na Tinubu: Sunayen Manya 17 Daga Cikinsu Ya Fito
An siye su da kuɗaɗe ne yayin zaɓen da ya gabata
Majiyar mu ta Tribune ta haƙaito Agbo ya na cewa abun ɓaƙin ciki ne irin yadda wakilan na jam'iyyar ta su suka siyar da jam'iyyar ta su gurin wasu jam'iyyun da su ke fafatawa da su a zaɓen ta hanyar karɓar kuɗaɗe, inda ya bayyana cewa babu wata jam'iyya da za ta lamunci irin wannan abu da suka yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ƙara da cewar abubuwan da wasu daga cikin shuwagabannin jam'iyyar a matakin jiha su ka yi baya ga zagon ƙasan da su ka yi wajen zaɓe, ya warware rantsuwar da suka yi a lokacin da su ke karɓar muƙamin.
Haka zalika kuma, kwamitin ayyuka na ƙasa na jam'iyar ya sanya wani kwamiti na ladabtarwa domin ya binciki ayyukan jam'iyyar a jihohi guda uku, wato jihar Edo, Delta da kuma jihar Ogun.
Shiri Ya Kwabe: Jigon Jam'iyya Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe
Sau biyu ana aika musu da goron gayyata ba su zuwa
Shugaban jam'iyyar na jihar Edo ya amsa gayyatar da jam'iyyar ta yi mi shi inda ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar, a yayin da abokanen aikin shi na jihar Delta da Edo suka ƙi amsa goron gayyatar da kwamitin ya aike musu har sau biyu.
Baya ga korar shuwagabannin da jam'iyyar ta NNPP ta yi a jihohin biyu, haka nan ma kwamitin ayyukan jam'iyyar ya sanar da rushe duka wasu muƙamai da jam'iyyar ke da su tun daga matakin jiha har ya zuwa na ƙananan hukumomi a jihohin biyu da abun ya shafa kamar dai yadda The Nation ta wallafa.
Lauyoyi 50 zasu kare Tinubu a gaban kotu
A wani labarin kuma, kun karanta cewa aƙalla lauyoyi 50 ne su ka shirya tsaf domin kare nasarar zaɓen sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa wato Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.
Hakan dai ya biyo bayan ƙin amincewa da sakamakon zaɓen da ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP Atiku Abubakar da kuma na Labour Party wato Peter Obi suka yi domin kuwa a cewar su ba Tinubu ba ne ya lashe zaɓen wanda hakan ya sa suka shigar da ƙara.
Asali: Legit.ng