Wike Na Yakar Cin Hanci Da Rashawa a Ribas, Inji Zababben Shugaban Kasa Tinubu
- Shugaban kasar Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu ya jinjinawa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
- Tinubu ya yaba ma Wike kan yadda yake yakar cin hanci da rashawa a jiharsa ta hanyar inganta rayuwar alkalai
- A cewar zababban shugaban kasar, tsarin da gwamnan na PDP ya dauko shine zai magance matsalar rashawa
Rivers - Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya jinjinawa gwamnan jihar Ribas, Nyesomn Wike, kan yakar cin hanci da rashawa da yake yi a jiharsa, jaridar Vanguard ta rahoto.
Yayin da yake kaddamar da ginin a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu, Tinubu ya ce alkawalai za su zama masu karbar rashawa idan suna aiki cikin talauci, don haka ya jinjinawa tsare-tsaren gwamnan na magance hakan.
Wike ya cancanci ayi koyi da shi, Tinubu
Ya ci gaba da bayyana cewar Wike ya yi abun da ya cancanci ayi koyi da shi inda ya nanata cewar"ba za ka sa ran alkalanku su zama cikin talauci, su yi aiki cikin talauci, sannan su yi adalci cikin talauci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ku yi duba da abun da Wike yake yi a yau ta wani bangare. Yana yaki da rashawa ne. Wannan shine hanyar yakar rashawa," in ji Tinubu.
Ya ci gaba da cewar:
"Ya zama dole mu yaki rashawa sannan ya zama dole mu duba daya bangaren silalla. Idan ba ku son alkalanku su zamo masu rashawa, ya zama dole ku mayar da hankali a bangaren jin dadinsu. Idan kuna son adalci, dole ka so su yi aiki a yanayi mai kyau. Mu yi maganar daraja da daraja."
Tinubu wanda ya kai ziyarar kwanaki jihar Ribas tun a ranar Laraba ya kuma kaddamar da gadar sama na Rumuola-Rumuokwuta wanda ke sada hanyar Rumuola zuwa Ikwerre, rahoton Leadership.
Tinubu ya ce Wike ya taimaka wajen nasarar da ya samu a zaben 2023
A wani labarin kuma, mun ji cewa Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasa ya ce ya samu nasara ne a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu saboda goyon bayan da ya samu daga bangaren gwamna Nyesom Wike na Ribas.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya amsa gayyatar Wike inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta yi a jihar Ribas.
Asali: Legit.ng