29 Ga Watan Mayu: Malaman Addini Sun Yi Barazanar Tsinewa Masu Neman a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi
- Wasu fastocin Najeriya daga jihar Ribas sun magantu a kan kiran da wasu ke yi na neman a kafa gwamnatin wucin gadi
- Fastocin da yawansu ya kai 100 sun yi barazanar yin tofin Allah tsine ga masu neman a ki rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu
- Sun ce duk masu neman kawo cikas ga tsarin damokradiyyar kasar za su gamu da fushin Allah
Rivers - Wata kungiyar fastoci daga jihar Ribas sun sha alwashin tsinewa duk mutanen da ke kira ga kafa gwamnati na wucin gadi a kasar, jaridar The Nation ta rahoto.
Malaman karkashin inuwar 'Rivers Pastors Unite for Tinubu (RPUT)' sun gargadi masu kiran a kan lalata damokradiyyar kasar cewa ya kamata su janye daga haka ko su gamu da fushin Ubangiji.
Fastoci 100 na shirin tsinewa masu son kafa gwamnatin wucin gadi
Fastocin da yawansu ya kai 100 sun bayyana matsayinsu a wata sanarwa da suka fitar a Port Harcourt a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu domin yi wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu maraba da zuwa jihar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar wanda jagororin kungiyar, Fasto Sunday Edimeh shugaban cocin One life Bible Church Port Harcourt da Fasto Julius Dan na cocin Apostolic Church of Nigeria suka saki ya ce su din masu goyon bayan shugabancin Tinubu/Shettima ne.
Sun ce sabanin abun da wasu suka yarda da shi, ba dukkanin fastoci ke adawa da nasarar Tinubu ba a zaben da ya gabata.
Sun ce a matsayinsu na kungiya wacce ba ta siyasa ba, sun hada kai ne kawai da tsarin Tinubu ta hannun tsohon kwamishinan ayyuka na Osun Injiniya Remi Omowaiye suna masu tuna cewa sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu tun kafin zabe, rahoton Punch.
Sun ce:
"Mu fastocin Ribas masu goyon bayan Tinubu, mun yi aiki sannan mun yi kamfen tare da mambobin cocinmu don nasarar Bola Tinubu. An yi mana shafen bakin fenti sannan aka kira mu da sunaye iri-iri amma godiya ga Allah, kokarinmu bai tashi a banza ba da nasarar Tinubu.
"Dalilinmu na goyon bayan Tinubu shine cewa tushensa ya nuna shine ya fi cancanta da aikin. Koda dai Musulmi ne shi, yana auren faston RCCG. Babu dan takarar shugaban kasa da ya marawa fastoci da malamai baya kamar Asiwaju Bola Tinubu.
"Daga cikin manyan mutanen da ya daukaka akwai mataimakin shugaban kasa (Fasto) Yemi Osinbajo, Fasto Tunde Fowler, tsohon shugaban FiRS, Fasto Ben Akabueze, Darakta Janar na ofishin kasafin kudin Najeriya da sauransu."
APC ta nesanta kanta daga ziyarar da Tinubu zai kai Ribas
A wani labari na daban, mun ji a baya cewa jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta bayyana cewa ziyarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai kai jihar Ribas bai da alaka da siyasa.
A cewar jam'iyyar mai mulki a kasar, ziyara ce ta gashin kai bisa gayyatar gwamnan jihar, Nyesom Wike amma ba wai ta hadaka tsakanin gwamnan da APC ba a jihar.
Asali: Legit.ng