Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Majalisar Dokokin Jihar Abiya Kan Rigimar da Ta Barke

Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Majalisar Dokokin Jihar Abiya Kan Rigimar da Ta Barke

  • Yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, sun garƙame wurin
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan wasu mambobin majalisar sun tsige kakakin majalisa, Honorabul Chinedum Orji
  • Tuni dai jami'an 'yan sandan suka kwace wurin kafin a shawo kan rikicin shugabancin da ya ɓalle

Abia - Jami'an hukumar 'yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Abiya dake Umuahia, babban birnin jihar ranar Talata 2 ga watan Mayu, 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan yunkurin wasu mambobin majalisar na tsige kakakin majalisar dokokin, Honorabul Chinedum Orji.

Zauren majalisar dokokin Abiya.
Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Majalisar Dokokin Jihar Abiya Kan Rigimar da Ta Barke Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mambobin majalisar sun zauna a wani wuri daban, sun shirya tsige shugaban majalisar bisa zargin rashin kula da walwalarsu.

A wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, wasu mambobin sun zauna sun sanar da tsige kakakin majalisa kana suka maye gurbinsa da Honorabul Chukwudi Apugo, mai wakiltar Umuahia ta gabas.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici Ya Barke, Yan Majalisa Sun Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda mambobin suka tunɓuke kakakin majalisar

Zaman yan majlisun ya gudana

karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisa, Ifeanyi Uchendu, mai wakiltar mazanar Ohafia ta kudu a inuwar jam'iyar PDP.

Honorabul Kennedy Njoku (Osisioma Ngwa ta arewa), ne ya gabatar da kudirin tsige kakakin kuma nan take ya samu goyon bayan Honorabul Chijioke Chukwu.

Wannan lamari dai ya haddasa sabon rikicin shugabanci a majalisar dokokin Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Duk wani kokarin jin ta bakin Sakataren watsa labarai na kakakin majalisar dokokin, Mista Jude Ndukwe, bai kai ga nasara ba.

Bai ɗaga kiran waya da kuma saƙonnin da aka tura wa lambar wayarsa kan batun tsige ubam gidansa ba har kawo yanzu ba muke haɗa muku wannan rahoton.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

Yan sanda sun kama Hudu Ari a Abuja

A wani labarin kuma tsohon kwamishinan zaben Adamawa ya shiga komar yan sanda a birnin tarayya Abuja

Tsohon kwamishinan zaben jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, na tsare a Ofishin yan sanda yanzu haka a birnin tarayya Abuja.

Wannan na zuwa ne mako biyu bayan Barista Ari ya yi layar bayan ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna a Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262