Shugaba Buhari Ya Isa Wurin Faretin Sojoji Sanye Da Kakin Soji

Shugaba Buhari Ya Isa Wurin Faretin Sojoji Sanye Da Kakin Soji

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya isa wurin Faretin sojoji a Eagle Square da ke Abuja sanye da kakin soji
  • A wasu Hotuna da hadimin shugaban kasan ya wallafa, an ga Buhari na zagayawa yana duba Sojoji 1000 da zasu yi Fareti
  • Manyan shugabannin tsaro a Najeriya da kusoshin gwamnatin tarayya sun halarci wurin yau Alhamis 27 ga watan Afrilu, 2023

Abuja - Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya isa wurin da jami'an rundunar soji zasu gabatar Faretin 2023 sanye da kakakin Soja.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya isa babban filin Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja, wurin da aka tsara gudanar da faretin da misalin ƙarfe 10:18 na safiyar Alhamis.

Shugaba Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari sanye da kakin soji a wurin fareti Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin kafafen sada zumunta na zamani, Buhari Sallau, ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa Hotunan Buhari.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10

Buhari ya isa babban filin da sojoji 1000 zasu gudanar da faretin bana tateda rakiyar shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ƙasa, Manjo Janar mai ritaya, ya sanya kayan biki na rundunar sojin Najeriya kuma a halin yanzu yana rangadin duba sojoji 1000 da suka ƙame a wurin faretin.

Shugabannin tsaro sun halarci wurin

Legit.ng Hausa ta faimci cewa shugaban jami'an tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor; shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya da Sufeta Janar na rundunar yan sanda, Usman Baba, sun je wurin Faretin.

Haka zalika shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao; shugaban rundunar sojin ruwa, da kuma Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, duk sun halarci wurin.

Bugu da ƙari, shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Ibarhim Lawan, na cikin manyan ƙusoshin gwamnatin Buhari da suka hallara a Eagle Square yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

Atiku Ya Ziyarci Babban Jigon Jam'iyyar APC, Sanata Orji Kalu

A wani labarin na daban kuma Atiku Abubakar Ya Ziyarci Sanatan APC Da Ke Neman Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sanata Orji Kalu, mai ladabtarwa a majalisar dattawa bisa rasuwar matarsa.

Sai dai ga dukkan alamu ba gaisuwa kaɗai ya je ba, domin Atiku da Kalu sun yi wata ganawar sirri a gidan tsohon gwamnan Abiya na Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262