Ministan Buhari Ya Faɗi Wanda Zai Iya Hana Rantsar da Tinubu a Watan Mayu

Ministan Buhari Ya Faɗi Wanda Zai Iya Hana Rantsar da Tinubu a Watan Mayu

  • Jigon jam'iyyar APC ya faɗi wanda ke da karfin ikon hana Bola Tinubu hawa kujerar shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu, 2023
  • Yayin da ake tunkarar bikin miƙa mulki, Festus Keyamo, ya ce Allah ne kaɗai zai iya dakatar da rantsar da Tinubu
  • Keyamo, ƙaramin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, ya ce jam'iyya mai mulki ba ta damu da yunkurin wasu yan adawa na hana bikin ba

Ƙaramain ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo (SAN) ya bayyana wanda ke da ƙarfin ikon dakatar da bikin miƙa mulki ga shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu.

Keyamo ya ce Allah mai girma da buwaya ne kaɗai idan ya so zai dakatar da rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Kasa da Wasu Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

Shettima da Bola.
Ministan Buhari Ya Faɗi Wanda Zai Iya Hana Rantsar da Tinubu a Watan Mayu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministan ya aike da sako ga masu son dakatar da Tinubu

Keyamo, babban jigo a jam'iyyar All Progressive Congress watau APC, ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ta shiga hannun Vanguard ranar Talata, 25 ga watan Afrilu, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin kwamitin kamfen Tinubu/Shettima wanda aka rushe kwanan nan, ya ce hankalin APC kwance ya ke game da rantsar da Bola Tinubu.

Keyamo ya ce:

"Me zai sa mu tsaya muna jin tsoro? Duk wani ɗan tsagin adawa da ke raye a yanzu, wanda ke ganin saboda wasu dalilan shari'a, ba za'a rantsar da Tinubu ba, lallai yana tunanin wawaye."
"Indai ba wani iko na Allah ba, wanda shi ne mai girma da buwaya, babu abinda zai hana rantsar da Asiwaju. Yan adawa na da zaɓi biyu, su maida hankali kan ƙarar da suka shigar ko su fara shirin tunkarar 2027."

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Mayu: Ministan Buhari Ya Bayyana Abu 1 Tal Da Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan shafe kusan wata guda a turai, inda ya tafi hutawa bayan kammala hayaniyar babban zaɓe.

Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Kasa da Wasu Jiga-Jigai

A wani labarin kuma Zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sa labule da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu

Taron wanda ya gudana a gidan da aka ware wa shugaban kasa mai jiran gado kuma a sirrance ya samu halartar manyan kusoshin jam'iyar APC.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da mataimakinsa na cikin waɗanda suka halarci ganawar a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262