Sanata Sani Musa Ya Musanta Janyewa Daga Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa

Sanata Sani Musa Ya Musanta Janyewa Daga Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Ɗaya daga cikin na kan gaba wajen fara neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, ya musanta cewa ya janye
  • Sanata Sani Musa ya ce har yanzu yana nan a kan bakar sa na ganin cewa ya ɗare kujerar shugabancin majalisar
  • Sanatan ya ce jam'iyyar APC kawai za ta iya kawo masa cikas ya haƙura da takarar shugabancin majalisar

Abuja - Sanata Sani Musa mai neman ɗarewa kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10, ya musanta cewa ya janye daga takarar, saɓanin rahotannin da ake yaɗa wa cewa ƴan takarar Arewacin Najeriya sun janyewa takwarorin su na Kudanci.

Musa, wanda ya ke wakiltar Niger ta Gabas yayi wannan ƙarin hasken ne a cikin sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce rahoton cewa ya janye ba shi bane ainihin halin da ake ciki a yanzu ba, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Bayan Kwanaki 33 a Kasar Waje, An Sanar da Lokacin da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya

Sani Musa ya musanta janyewa daga takara
Sanata Sani Musa, sanata mai wakiltar Niger ta Gabas Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Musa ya bayyana cewa dalilin da kawai zai sanya ya janye shine idan shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress ta yanke shawarar kai shugabancin majalisar a wani yanki wanda ba yankin Arewa ta tsakiya ba.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hankali na ya kai kan wani labari cewa ɓa haƙura da burin zama shugaban majalisar dattawa ta 10."
"Ina zaton wannan tunanin marubucin da ya rubuta labarin a wannan jaridar ne."
"Har yanzu ina cikin takara sannan zan yanke abinda ba hakan bane kawai idan tsarin jam'iyyar mu bai sanya kujerar shugaban majalisar dattawa ko mataimakin ba ta faɗo yanki na ba."
"Ina kira ga zaɓaɓɓun sanatoci ƴan'uwa na, mutanen mazaɓata da sauran al'umma da su cigaba da jajircewa da fatan samun majalisa ta 10 wacce za ta ci gashin kanta kuma abokiyar aiki ga gwamnatin mu mai kamawa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zabaɓben Ɗan Majalisar Tarayya Dan Shekara 36 Ya Rasu Ana Tsaka da Shagalin Sallah

Sanata Musa ya kuma nuna aniyar sa ta karɓar kujerar mataimakin shugaban majalisar, idan ba a kai kujerar shugabancin majalisar yankin sa ba, cewar rahoton Thisday.

Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Kasar Waje

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa shugaba Buhari zai shilla zuwa ƙasar Ghana domin halartar wani muhimmin taro na shugabannin ƙasashen yankin Guinea.

Za a gudanar da taron ne a birnin Accra na ƙasar Ghana, kuma shugaɓa Buhari na daga cikin masu jawabi a taron

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng