Zulum: Na Ji Daɗi Kasancewa Tinubu Da Shettima Ne Za Su Gaji Buhari

Zulum: Na Ji Daɗi Kasancewa Tinubu Da Shettima Ne Za Su Gaji Buhari

  • Zulum ya ce hankalinsa ya kwanta da ya kasance Tinubu da Shettima ne za su gaji Buhari
  • Gwamnan Jihar Borno ya ce yana farin ciki kasancewar maigidansa Shettima ya zama zababben mataimakin shugaban kasa
  • Zulum, a liyafar cin abincin idi da aka shirya a gidan gwamnati ya ce tun 2019 ya ke addu'ar Kashim ya zama mataimakin shugaban kasa

Borno - Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno, ya ce ya na farin ciki da ya kasance Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, da Kashim Shettima, zababben mataimakin shugaban kasa, sune za su gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Zulum ya bayyana haka ranar Juma'a yayin layifar cin abincin idi a gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, rahoton The Cable.

Zulum da Shettima
Zulum: Na Ji Dadi Kasancewa Tinubu Da Shettima Ne Za Su Gaji Buhari. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Hankali na ya kwanta ganin Tinubu da Shettima za su gaji Shugaba Buhari, In Ji Zulum

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Zulum ya bayyana nasarar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa a matsayin kwanciyar hankali gare shi da gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Babban abin farin ciki ne a gare mu yau, ga Kashim Shettima a zaune cikinmu a matsayin zababben mataimakin shugaban kasa mai jiran rantsuwa. Abin da na dinga addu'a tun da aka rantsar da ni a 2019.
"A bangare guda, Shugaba Buhari ya kasance mafi bada goyon baya wajen magance matsalolin Jihar Borno.
"A gaskiya yana daga cikin abun da ya ke hana ni bacci. Insha Allah a shekaru hudu masu zuwa zan kasance tare da dan uwana, kuma maigidana da zai tallafa min da kuma tallafawa gwamnatin mutanen Jihar Borno. Muna da shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu da ke matukar kaunar Borno ya kuma damu da matsalolinmu."

A baya bayan nan Zulum ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin babban jigo gare shi tsawon shekara hudu a wa'adinsa na farko.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Ya ce shugaban kasar ya ba shi kyakkyawar gudunmawa wajen yaki da yan Boko Haram da taimakawa ayyukan tallafawa dan adam da cigaban Borno.

Zulum Zai Sake Gina Kauyuka Uku Da Aka Lalata Bayan Buhari Ya Ba Shi N15bn

A wani rahoton, gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da niyyarsa na sake fara aikin ginin wasu kauyuka uku da yan Boko Haram suka lalata a yankunan jihar.

Zulum ya ce zai taimaka domin ganin cewa yan gudun hijira da suka bar gidajensu sun koma domin cigaba da rayuwarsa kamar yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164