Na Yi Mamakin Yadda Iyalaina Suka Zabi Peter Obi, Gwamna Umahi
- Gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana yadda ya sha mamaki a babban zaɓen shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023
- David Umahi na jam'iyyar APC ya ce wasu daga cikin iyalansa ba su tsaya a inuwarsa ba, Peter Obi suka zaɓa
- Ya ce kuri'un da LP ta samu ba don Peter Obi bane, mutane sun ƙaurace wa APC ne saboda halin da suka tsinci kansu
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana yadda iyalan gidansa suka haɗa baki suka guje masa a ranar zaɓen shugaban kasa 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Gwamnan na jam'iyyar APC ya ce iyalansa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, suka dangwala wa kuri'unsu maimakon Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Umahi ya yi wannan furucin yayin da yake jawabi kan kulla makirci da haɗin baki a cikin wata hira da Channels tv ranar Litinin 17 ga watan Afrilu, 2023.
Ya ce abun ban mamaki ne yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, suka sha kashi a jihohinsu a zaben 25 ga watan Fabrairu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Umahi, zaɓaɓɓen Sanatan Ebonyi ta kudu, mutane sun kaɗa wa LP kuri'unsu ba don Peter Obi ne ɗan takara ba, sai don nuna fushinsu kan kunci da wahalhalun da suke fama da su.
A kalamansa ya ce:
"A zahirin gaskiya, ban bar ƙofa ko ɗaya da zata baiwa Labour Party damar cin zaɓe a jihata ba saboda abubuwan da muka zuba a ƙasa ba zasu bar kowace jam'iyya ta ci komai ba ko zaɓen Kansila a jihar."
"Ina ganin LP ta samu kuri'u ne saboda mutane su nuna fushinsu kan jam'iyyata APC da kuma PDP. Na sha mamaki, har a cikin iyalina, wasu sun haɗa baki sun guje ni."
"Ban san Peter Obi suka zaɓa ba amma a sauran zabuka sun zabi jam'iyyar APC saboda abubuwan da muka yi a jihar. Ƙuri'un ba na Peter Obi bane kai tsaye, ana fama da rayuwar ƙunci da kalubale a Najeriya."
A wani labarin kuma Kwamishinonin Hukumar Zabe INEC Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja Kan zaben Adamawa
Yayin da ake ta cece kuce kan abinda ya faru a jihar Adamawa, kwamishinonin zabe na faɗin Najeriya sun taru a Abuja don tattauna batun.
Rahotanni sun nuna cewa REC ɗin sun sa labule domin tattauna matakin da ya kamata su ɗauka kan takwaransu da ya aikata abinda ya faru.
Asali: Legit.ng