Gwamna Makinde Ya Gana da Fintiri a Adamawa, Ya Roki INEC Abu 1

Gwamna Makinde Ya Gana da Fintiri a Adamawa, Ya Roki INEC Abu 1

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ziyarci takwaransa na jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a Yola ranar Litinin
  • Makinde ya roki hukumar zaɓe ta kasa ta yi abinda ya dace wajen bayyana sahihin wanda ya ci zaɓen Adamawa
  • Kwamishinan INEC na jihar ya bar baya da ƙura biyo bayan ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta ci zaɓe

Adamawa - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya roki hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Adamawa.

Makinde ya yi wannan roko ne yayin da ya gana da takwaransa na Adamawa, Ahmadu Fintiri, lokacin da ya kai masa ziyarar ana tare gidan gwamnati da ke Yola ranar Litinin.

Gwamna Seyi Makinde.Da Fintiri
Gwamna Makinde Ya Gana da Fintiri a Adamawa, Ya Roki INEC Abu 1 Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Kwamishinan INEC ya ta da ƙura

Idan baku manta ba kwamishinan zaɓen jihar, Hudu Yunusa Ari, ya shiga ruɗun bayyana Aishatu Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, INEC Ta Hukunta Kwamishinan da Ya Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan abu da REC ya aikata ya ta da ƙura, inda jam'iyyun siyasa da masu kishin ƙasa suka yi tir da lamarin. Haka nan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yi Alla-wadai, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Yayin ɗaukar mataki kan lamarin, INEC ta dakatar da tattara sakamakon kana ta umarci Ari ya nesanta kansa daga harkokin hukumar da kuma zaɓen Adamawa.

Za'a warware matsalar - Makinde

Channels tace yayin wannan ziyara, Makinde ya yi kira ga mutanen jihar Adamawa su kwantar da hankulansu kuma ya tabbatar da cewa za'a magance matsalar da ta taso.

Gwamna Makinde na Oyo ya bayyana sanar da yar takarar APC a matsayin wacce ta lashe zabe ba kan ƙa'ida ba da abin kunya ga mutum kamar Ari kuma ba'a yi tsammani ba.

Bugu da ƙari, Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Aminu Tambuwal ta yi Allah wadai da baiwa Binani Nasara, inda ta kira lamarin da abun kunya a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Jam'iyyar PDP Ta Shiga Zanga-Zanga, Ta Sha Wani Muhimmin Alwashi Kan INEC

A wani labarin kuma Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamnan APC Uku da Jam'iyyar Ta Miƙa wa INEC

Bayan kammala zaben fidda gwani a jihohin Najeriya uku, jam'iyya mai mulki ta miƙa sunayen yan takararta ga hukumar zaɓe INEC.

A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi, Imo da kuma Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262