Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Yan Majalisu 8 a Cikon Zaben Jihar Kebbi

Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Yan Majalisu 8 a Cikon Zaben Jihar Kebbi

  • Jam'iyyar APC ta samu nasara a mafi yawan cikon zaben mambobin majalisar dokokin jihar Kebbi da aka kammala
  • INEC ta ayyana yan takarar jam'iyya mai mulki a matsayin waɗanda suka samu nasara a mazabun yan majalisa 8
  • Ɗan takarar APC ne ya samu nasarar lashe zaben gwamna a jihar Kebbi kamar yadda baturen zaɓe ya sanar

Kebbi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu nasarar lashe kujerun mambobin majalisar dokokin jiha guda 8 a zaɓen da aka ƙarisa a jihar Kebbi.

Jami'ai masu alhakin tattara sakamako a waɗannan mazaɓu guda 8 ne suka sanar da haka a zaurukan haɗa sakamakon da daren Lahadi, 16 ga watan Afrilu, 2023.

Tutar jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Yan Majalisu 8 a Cikon Zaben Jihar Kebbi Hoto: OfficialAPC
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mazaɓun da APC ta ci kujerunsu sun ƙunshi, Arewa, Augie Gwandu, Jega, Kalgo, Koko Besse, Maiyama da kuma Sakaba.

Kara karanta wannan

Binani Vs Fintiri: Jerin Muhimman Abubuwan Sani 9 Kan Halin Da Ake Ciki Dangane Da Zaben Gwamnan Adamawa

Tun da fari INEC ta ayyana zabukan waɗan nan yan majalisu a matsayin wanda bai kammalu ba a zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar jihohi wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta gano cewa kawo yanzu hukumar ta ayyana sakamakon zaɓe a mazabun mambobin majalisar dokokin jihar Kebbi 11 yayin da ake dagon matakin da INEC zata ɗauka game da zaɓen Yauri da Ngaski.

A ranar Asabar da ta shige 15 ga watan Afrili, 2023, INEC ta gudanar da cikon zaɓen gwamna a jihar Kebbi da Adamawa da kuma wasu mazaɓun 'yan majalisar jiha da na tarayya a sassan ƙasar nan.

Hakan ya biyo bayan ayyana zabukan da waɗanda basu kammalu ba sakamakon tazarar da ke tsakanin na ɗaya da na biyu ba ta kai yawan kuri'un da aka soke ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

INEC Ta Yanke Hukunci Kan Kwamishinan da Ya Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa

A wani labarin kuma Hukumar zabe INEC ta dakatar da kwamishinanta na jihar Adamawa har sai baba ta gani

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin 17 ga watan Afrilu, ya umarci REC ɗin ya nesanta kansa da harkokin zaɓen jihar Adamawa.

Bayan haka ta umarci sakataren gudanarwa ya maye gurbinsa nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262