INEC Ta Umarci Hudu Ari Ya Tsame Hannunsa Daga Zaben Adamawa

INEC Ta Umarci Hudu Ari Ya Tsame Hannunsa Daga Zaben Adamawa

  • Hukumar zaɓe INEC ta umarci kwamishinanta na jihar Adamawa, Barista Hudu Ari, ya nesanta kansa daga harkokin zaɓen jihar
  • Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan REC ɗin ya yi gaban kansa ya ayyan Binani a matsayin gwamna
  • Lamarin dai ya haddasa cece kuce a faɗin ƙasar nan kuma tuni INEC ta soke kalaman REC ɗin domin ba shi da hurumi

Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ɗauki tsattsauran mataki kan kwamishinan zaɓe (REC) na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari.

Channels tv ta rahoto cewa INEC ta umarci Hudu Ari ya tsame hannu kuma ya nesanta kansa daga dukkan harkokin hukumar da kuma zaɓen jihar Adamawa.

Bar Ari.
INEC Ta Umarci Hudu Ari Ya Tsame Hannunsa Daga Zaben Adamawa Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da INEC ta aike wa kwamishinan mai ɗauke da sa hannun Sakatare, Rose Oriaran Anthony, ranar 17 ga watan Afrilu, 2023.

Kara karanta wannan

Binani Vs Fintiri: Jerin Muhimman Abubuwan Sani 9 Kan Halin Da Ake Ciki Dangane Da Zaben Gwamnan Adamawa

Sanarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina mai sanar maka (Barista Hudu Yunusa Ari) kwamishinan zaɓe a Adamawa cewa hukuma ta yanke ka yi nesa da ofishinta na Adamawa nan take har sai baba ta gani."
"Kuma ta umarci Sakatare ya maye gurbinka a Adamawa nan take."

Abinda ya faru

Barista Ari, kwamishinan da ya jagoranci zaben gwamna a jihar Adamawa ya haddasa ruɗani da safiyar Lahadi bayan ya ayyana Aishatu Binani, yar takarar APC a matsayin wacce ta samu nasara.

Wannan sanarwa da Ari ya yi ta haddasa ruɗani kuma ya wuce gona da iri a ƙarfin ikon da kundin mulkin Najeriya ya rataya masa.

Baya ga shiga hurumin Baturen zabe wanda shi ke da alhakin sanar da sakamakon, Ari ya ƙara kwafsawa wajen sanar da sakamakon zaɓen da ba'a gama tattarawa ba.

Kara karanta wannan

Adamawa: Hukumar INEC Ta Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Ayyana Binani a Matsayin Sabuwar Gwamna

A martanin da ta yi cikin hanzari, INEC ta soke matakin ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓe kuma ta ɗage ci gaba da tattara sakamakon.

INEC Ta Nesanta Kanta Daga Sanar Da Samun Nasarar Binani

A wani labarin kuma Hukumar INEC Ta Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Ayyana Binani a Matsayin Sabuwar Gwamna

INEC ta yi fatali da sanar da Sanata Aishatu Ɗahiru Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262