Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP Ta Shiga Zanga-Zanga a Adamawa, Ta Sha Wani Muhimmin Alwashi

Wata Sabuwa: Jam'iyyar PDP Ta Shiga Zanga-Zanga a Adamawa, Ta Sha Wani Muhimmin Alwashi

  • Jam'iyyar PDP a Jihar Adamawa ta tsunduma zanga-zanga kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa
  • Jam'iyyar ta PDP tana neman dole sai hukumar zaɓe ta dawo ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Masu gudanar da zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da yin ta har sai sun ga abinda ya turewa buzu naɗi

Jihar Adamawa - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta fita kan tituna zanga-zangar nuna adawa da bayyana Aisha Dahiru Binani, a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Daily Trust tace kwamishinan zaɓen hukumar INEC na jihar, Barista Hudu Ari, a ranar Lahadi ya bayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen, ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen cike gurbin gwamnan da aka yi ranar Asabar.

PDP ta shiga zanga-zanga a Adamawa
Magoya bayan PDP masu zanga-zanga a jihar Adamawa Hoto: Pulse.com
Asali: UGC

Zanga-zangar ta ranar Litinin ta fara ne daga ofishin jam'iyyar PDP da ke kusa da gadar masu tafiya a ƙasa, sannan ta ƙare a hedikwatar hukumar zaɓe ta INEC da ke a Dougerei, cewar rahoton Pulse.ng

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Doke Manyan Abokan Karawarta, Ta Lashe Ƙarin Kujerun Yan Majalisa 8

Da ya ke jagorantar zanga-zangar, mataimakin darektan kamfen ɗin gwamnan PDP na jihar, Felix Tangwama, ya ce za su ci gaba da zanga-zangar har sai an dawo an ci gaba da tattara sakamakon zaɓen sannan an bayyana sakamakon zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Al'ummar Adamawa na neman da a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen domin samun zaman lafiya a Adamawa."
"Ba mu ji daɗin abinda Hudu da masu goya masa baya suka yi ba. Waɗanda yakamata ace suna tabbatar da doka wai sune a zaune tare da shi. Wannan abin kunya ne, ya saɓa doka kuma abin Allah wadai ne, sannan duk masu hannu a ciki yakamata a hukunta su."
"Saboda haka, mun fito nan domin gudanar da zanga-zanga sannan muna tabbatarwa da INEC cewa za mu ci gaba da zanga-zanga kullum har sai an cigaba da tattara sakamakon zaɓe.

Kara karanta wannan

Binani Vs Fintiri: Jerin Muhimman Abubuwan Sani 9 Kan Halin Da Ake Ciki Dangane Da Zaben Gwamnan Adamawa

“Sakamakon zaɓen yana kan IReV, sannan za mu so ganin wani irin siddabaru za a yi amfani da shi domin sauya sakamakon zaɓen da ke akan fotal ɗin INEC."

Abubuwan Sani Dangane Da Halin Da Ake Ciki Kan Zaben Gwamnan Adamawa

A wani rahoton na daban, kun ji yadda mu ka yi duba kan wasu muhimman abubuwan sani dangane da halin da ake ciki kan zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Zaben gwamnan na jihar Adamawa ya bar baya da ƙura, inda ya kasance cike da ruɗani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng