Zaben Majalisa: Wasu Mutum 2 Su na Raba Cin Hancin N460m Inji Gwamnonin APC
- Zargin da ake yi shi ne ‘Yan takaran majalisar tarayya su na ba takwarorinsu cin hancin Daloli
- Gwamnonin jam’iyyar APC sun rubuta wasika domin ankarar da Bola Tinubu abin da ke faruwa
- Akwai mutum biyu da suka shirya batar da tsakanin $500, 000 zuwa $1m domin samun mukami
Abuja - Wasu mutane biyu da suke neman zama shugaban majalisar wakilai da shugaban majalisar dattawa su na bada cin hanci domin su yi nasara.
Rahoton da aka samu daga Premium Times dazu ya tabbatar da ‘yan majalisar nan su na kashe har Dala miliyan 1 domin samun kuri’un abokan aikinsu.
Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun rubuta takarda zuwa ga Bola Tinubu wanda zai karbi shugabanci a karshen Mayu.
Abin da takardar Gwamnonin ta kunsa shi ne zargin cewa akwai wani ‘Dan majalisar wakilai da Sanata da ke facaka domin samun shugabanci.
Rade-radin cin hanci su na yawo
Kungiyar PGF ta Gwamnonin ta ce ta samu rade-radin masu neman zama Shugaban majalisar wakilai da na Dattawa su na bada $500, 000 zuwa $1m.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng Hausa ta fahimci wadannan kudi sun tashi tsakanin N230m zuwa N460 a kasuwar canji.
Wasikar Gwamnonin APC
"Ta tabbata, ana jita-jita cewa daya daga cikin masu neman zama shugaban majalisar dattawa da mai neman shugabancin majalisar wakilai sun shirya batar da $500, 000 zuwa $1m a kan kowane kuri’a.
Ana bin ‘yan adawa a majalisar tarayya, idan ba ayi sake ba abin da zai faru a 2015 zai maimaita kan shi."
- Wasikar PGF
Ina mafita?
Rahoton ya kara da cewa kungiyar ta roki zababben shugaban kasar ya dauki mataki ta hanyar ware kujerun majalisar tarayyar ga kowane yanki na Najeriya.
Gwamnonin sun kawo shawarar yadda ya kamata ayi kason kujeru da mukaman domin a raba gardama, a san wadanda za su nemi takarar da za a shiga.
Nairaland ta ce Gwamnonin ba su iya kama sunan ‘yan majalisar da ke neman kujerun ido rufe ba, sai dai sun tabbatar da ‘yan jam’iyyarsu ne da aikin.
Zargin magudin zabe a Ribas
Da alama magoya bayan Peter sun yi gaskiya da suka ce an yi masu magudi a Jihar Ribas, wani rahoto da muka samu yana kokarin tabbatar da zargin na su.
Bincike ya nuna an rika canza sakamakon zaben da aka yi a Ribas domin Bola Tinubu ya yi nasara. Dama Gwamna Nyesom Wike ya yaki jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng