Nasir Idris: Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi
A ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress ( APC), Dr Nasiru Idris, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi.
Baturen zaben gwamna a jihar, Farfesa Sa'idu Yusuf, ya ce dan takarar na APC ya lashe zaben da kuri'u 409,225 wajen lallasa abokin hamayyarsa, Aminu Bande na PDP wanda ya samu kuri'u 360940, Daily Trust ta rahoto.
A lokacin zaben gwamna na 18 ga watan Maris, INEC ta ayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammalu ba saboda barkewar rikici da zarcewar kuri'u da aka kada.in
Ga jerin abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da zababben gwamnan:
1. An haifi Dr. Nasir Idris wato Kauran Gwandu a jihar Kebbi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Ya kasance shahararren mai ilimi kuma dan kungiyar kwadago
3. Ya mallaki digiri na uku a bangaren ilimi kuma ya wallafa litattafai da dama kan ilimi da bangarori masu alaka.
4. Idris ya fara aiki a matsayin malami sannan ya dungi dagawa har zuwa matakin shugaban kungiyar malamai na Najeriya (NUT), mukamin da yake rike da shi a yanzu.
5. Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kungiyar kwadago na Najeriya.
6. Yan Najeriya da dama da ke kallonsa a matsayin wanda ya cancanta kuma gogaggen shugaba wanda zai iya kawo ci gaba sun yaba da zamowarsa dan takarar gwamnan APC a Kebbi.
7. Idris na da matar aure da yara.
Atiku ga INE: "Ku gaggauta komawa kan tattara sakamakon gwamnan Adamawa"
A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC da ta gaggauta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa.
Atiku ya zargi hukumar zaben da kokarin murde muradin al'ummar jihar Adamawa ta hanyar ayyana yar takarar gwamnan na jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan ta kowani hali.
Ya kuma bukaci a kama duk wadanda ke kokarin cin amanar kasa da take tsarin damokradiyya a zaben.
Asali: Legit.ng