Yan Daba Sun Kai Hari Rumfar da Ake Zabe Yau a Jihar Kano
- Wasu yan daba adadi mai yawa sun tarwatsa mutane a wurin cikon zaɓen da ke gudana a wata rumfa a jihar Kano
- Rahoto ya nuna cewa ɗaruruwan yan daban sun fara ruwan duwatsu, lamarin da ya tilastawa mutane gudun neman tsira
- Sai dai nan take jami'an yan sanda suka maida martani, suka fatattaki maharan aka ci gaba da kaɗa kuri'a
Kano - An fara kaɗa kuri'a a wata rumfar zaɓe da ke gundumar Alasawa Kwaciri mai lamba 030, yankin Kurna Gabas a karamar hukumar Fagge, jihar Kano amma yan daba sun ta da hayaniya.
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa malaman zaɓe sun kimtsa kuma har anfara kaɗa kuri'a amma ɗaruruwan tsagerun 'yan daba ɗauke da muggan makamai suka tarwatsa mutane.
An hangi masu kaɗa kuri'a maza da mata suna gudun neman tsira da rayuwarsu daga mugun nufin 'yan daban, waɗanda suka fara ruwan duwatsu kan duk wanda ya tsaya.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Sai dai nan take jami'an tsaro suka kai ɗauki kuma suka taka wa yan daban birki komai ya dawo kan hanya aka ci gaba da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta faminci cewa Jami'an rundunar 'yan sanda ɗauke da makaman aiki sun fatattaki 'yan daban daga wurin, suka samar da ingantaccen tsaro a rumfar.
Zuwan jami'an yan sandan ne ya zama kariya ga kayayyakin zaɓen da ma'aikatan wucin gadi na INEC daga mugun nufin maharan.
Bayan yan sanda sun saita komai kuma sun baiwa malaman zaɓe kariya, sai suka fara kiran masu kaɗa kuri'a su dawo su dangwalawa wanda ransu ke so.
Tuni dai zabe ya kankama a yankunan da ya kamata yau Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023 ranar gudanar da cikon zaɓe, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.
Yan Daba Sun Sace Akwatun Zabe
A wani labarin kuma Yan Daba Sun Sace Akwatun Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi a jihar Imo Yau Asabar a Gaban Jami'an tsaro
Ganau ya bayyana cewa abun da ban mamaki yadda cikin sauki 'yan daban suka tafi da akwatin duk da kayan aiki da tulin jami'an tsaron da aka girke a rumfar.
Asali: Legit.ng