Zaben Cike Gurbi: “Ganduje Ya Yo Hayar Yan Daba”, Abba Gida-Gida Ya Koka
- Sabon takaddama ya kunno kai yayin da ake shirin zaben cike gurbi a jihar Kano wanda za a yi a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu
- Zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya koka cewa akwai kulla-kulla da ake yi don tarwatsa tsarin zaben
- Ya ce gwamnan jihar mai ci, Farfesa Abdullahi Ganduje ne ke shirya wannan makarkashiyar
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kara shiga sabon takaddama bayan zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi sabon zargi a kansa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Abba gida-gida ya yi zargin cewa Ganduje ya rabawa shugabannin kananan hukumomi tsabar kudi na miliyoyin naira gabannin zaben cike gurbi da za a yi a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu a jihar Kano.
Abba ya bayyana zarginsa a cikin wata sanarwa da aka gabatarwa manema labarai ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar na cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"An saki kudin ne don daukar nauyin yan dabar siyasa domin su tayar da zaune tsaye kan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da mazauna jihar Kano yayin zaben cike gurbi.
"Muna so mu sake gargadin shugabannin kananan hukumomi da ma'aikatansu ciki harda daraktoci, masu kula da harkokin kudi da sauran ma'aikata a matakin jiha da kananan hukumomi da ke da hannu a lamarin kai tsaye ko a kaikaice da su janye kansu sannan su tabbatar da cewa dukka kudaden da za a saki ba a yi amfani da su a kan irin wannan manufofi ba sannan a mayar da su asusun da ya dace."
Abba Gida-Gida ya yi kira ga hukumomin tsaro da su shigo lamarin
Kamar yadda ya zo a cikin sanarwar, Abba Yusuf ya yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin da ya dace don hana duk wani abu da ke neman kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma a yayin gudanar da zaben cike gurbin.
An kuma tattaro cewa Ganduje ya dauki hayar yan daba a ciki da wajen Kano domin su tarwatsa tsarin zaben.
Daily Trust ta rahoto cewa wannan na daya daga cikin jerin shawarwarin da zababben gwamnan ya bayar tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.
A nashi bangaren, Ganduje ya sha fada masa cewa ya guji yin kalamai na zagin gwamnati mai ci.
An kori jami'an yan sandan da ke tsaron Rarara
A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya ta kori jami'anta uku da ke ba mawakin siyasa, Dauda Katuhu Rarara tsaro.
Asali: Legit.ng