Ana Dab Da Zabe, PDP Ta Bankado Shirin Yi Wa Dan Takarar Gwamnanta Magudi a Adamawa
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bugi ƙirjin cewa ta shirya tsaf domin tunkarar zaɓen cike gurbi na gwamnan Adamawa
- Jam'iyyar ta kuma koka kan yadda aka ƙi sauraron koken da ta shigar kan kwamishinan zaɓen INEC na jihar
- PDP ta yi kira ga magoya bayan ta da su fito su yi wa ɗan takarar gwamnan ta ruwan ƙuri'u a zaɓen
Jihar Adamawa - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Adamawa ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar na ranar Asabar da zummar lashe zaɓen.
Jam'iyyar ta haƙiƙance cewa ba zata zura ido ba ta bari wasu marasa kishi su yi wa ɗan takarar gwamnan ta murɗiya ba a zaɓen amma zata yi duk abinda doka ta yarda da shi domin kare ƙuri'un ta, cewar rahoton Vanguard
Da yake magana da manema labarai a birnin Yola, darekta janar na kamfen ɗin jam'iyyar PDP, Awwal Tukur, ya bayyana cewa jam'iyyar ta shigar da ƙorafe-ƙorafe akan kwamishin zaɓen INEC na jihar amma an yi kunnen uwar shegu da su.
Ya bayyana cewa jam'iyyar zata sanya ido akan dukkanin kayayyakin zaɓen domin tabbatar da gaskiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga nan sai yayi kira da magoya bayan jam'iyyar da su fito kwan su da ƙwarƙwatar su domin zaɓen ɗan takarar jam'iyyar sannan su tabbatar sun tsare ƙuri'un su, rahoton Hotpen ya tabbatar.
Masu sa ido sun yi Allah wadai da kiran a cire kwamishinan INEC
A halin da ake ciki, gamayyar masu sanya ido kan zaɓe na cikin gida sun yi Allah wadai da ɗabi'ar wasu ƴan siyasa ta shirya zanga-zanga don kiran a cire kwamishinan zaɓen INEC na jihar.
Shugaban gamayyar masu sanya idon ya bayyana cewa ba a yin nasara a zaɓe ta hanyar farfaganda inda ya ƙara da cewa sun tura masu sa ido mutum 153 domin zaɓen cike gurbin na ranar Asabar.
Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Da Mataimakinsa a Jihar Legas
A wani rahoton na daban kuma, jam'iyyar PDP ta dakatar shugaban jam'iyyar da mataimakinsa a jihar Legas.
Jam'iyyar ta dakatar da shugabannin ne bayan ta zarge su da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa a lokacin zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris 2023.
Asali: Legit.ng