Zaben Gwamnan Kano: Abba Gida-Gida Kuri'a 178,374 Ya Samu Ba Miliyan 1 Ba, APC Ta Fada Wa Kotu
- Jam'iyyar APC ta shigar da kara gaban kotun kararrakin zabe ta na neman a ayyana dan takararta a matsayin wanda ya lashe zabe
- Jam'iyyar ta APC ta bukaci a sake bibiyar takardun kada kuri'a a kananan hukumomin jihar 32 in ta ke zargin an yi amfani da takardar kada kuri'a ta bogi
- A karar da ta shigar da hukumar zabe INEC da dan takarar NNPP, APC ta ce halastattun kuri'u 178,374 Abba ya samu a zaben
Jihar Kano - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Jihar Kano ta ce Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna na NNPP, kuri'a 178,374 kacal ya samu a zaben gwamnan jihar, The Cable ta rahoto.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben bayan samu kuri'a 1,019,602 wanda ya kada babban abokin hamayyarsa Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'a 890,705.
Jerin Yan Takarar Shugaban Kasa Da Jam’iyyun Da Ke So Kotu Ta Tsige Tinubu a Matsayin Zababben Shugaban Kasa
A karar da ta shigar gaban kotun kararrakin zabe, APC ta ce Abba bai cinye zabe da mafi rinjayen halastattun kuri'u ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ta ce "haramtattun takardun kuri'a" da ba sa hannu, tambari ko kwanan wata aka yi amfani da su a kananan hukumomi 32 daga cikin 44 a fadin jihar lokacin zaben.
"Wanda ake kara na biyu (Yusuf) bai ci zabe da mafi rinjayen halastattun kuri'un da aka kada ba a zaben" APC ta bayyana a cikin karar.
"Mai kara ya maimaita sakin layi 1-83 na karar don ya zama hujja akan wanda ake kara na biyu bai lashe zabe da mafi rinjayen kuri'a ba."
Ta cigaba da cewa:
"Mai kara ya cigaba da cewa a zaben da aka gudanar na kujerar gwamnan Kano da aka yi ranar 18 ga watan Maris 2023, an yi amfani da takardun kada kuri'a da basa dauke da sa hannu da kwanan wata don zabar wanda ake kara na biyu a kananan hukumomin da aka zayyana.
Kitimurmura: Kotu ta soke wasu tarukan zaben APC da aka yi a jihar Arewa don zabo dan takarar gwamna
"Saboda haka mai kara na neman wanda ake kara na daya da a sake kirga takardun kuri'a da aka yi amfani da su a kananan hukumomin da abin ya shafa a Jihar Kano kamar yadda mu ka bukata.
"Mai kara ya ce idan aka kwashe haramtattun kuri'un wanda ake kara na biyu da yawan su ya kai 896,022 daga cikin jamillar sakamakon da aka bayyana wanda ake kara na biyu zai samu kuri'a 178,374 yayin da mai kara da dan takararta su ke da mafi rinjayen halastattun kuri'u 890,705 kuma ya kamata a bayyana su a matsayin wanda su ka yi nasara a zaben."
Abba Gida-Gida: Zan yi mulki daidai da muradin al'ummma
A wani rahoton kun ji cewa zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai fifita abubuwan da suka shafi cigaban al'umma da samar da ilimi da zarar an rantsar da shi.
Asali: Legit.ng