Majalisa Ta 10: Jerin Jiga-Jigan 'Yan Majalisar Da Ke Neman Shugabancin Majalisar Dattawa

Majalisa Ta 10: Jerin Jiga-Jigan 'Yan Majalisar Da Ke Neman Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Ƴan majalisar dattawa da dama sun shiga cikin jerin masu neman shugabancin majlisar dattawa ta 10
  • Tun kafin a rantsar da sabuwar majalisar dattawan ta 10, ƴan majalisu sun fito fili sun nuna maitar su don samun shugabancin majalisar
  • Majalisar dattawan ta 10 zata fara ne aiki ne a watan Yuni bayan an rantsar da Asiwaju Bola Tinubu

FCT, Abuja - A yayin da ake shirin rantsar da majalisar dattawa ta 10, zaɓaɓɓun ƴan majalisa da dama sun fara neman kujerar shugabancin majalisar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, za a rantsar da sabuwar majalisar ne a cikin watan Yunin 2023, bayan an rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Jerin yan majalisar dattawa masu neman shugabancin majalisa ta 10
'Yan majalisar dattawa yayin zaman majalisa Hoto: Vanguard.com
Source: UGC

Majalisar dattawan ta 10 zata cika ne da ƴan majalisun da suka fito daga jam'iyyun All Progressives Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP) da New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya Da Ta Tsamo Daga Kangin Talauci a 2022

Sauran jam'iyyun sun haɗa da Social Democratic Party (SDP), All Progressives Grand Alliance (APGA) Young Peoples Progressive Party (YPP).

Tuni dai aka fara neman shugabancin majalisar dattawan tun kafin a rantsar da ita.

Ana kyautata zaton cewa zaɓen sabon shugaban majalisar dattawan zai zo ne ta hanyar tsarin karɓa-karɓa na jam'iyyar APC mai mulki.

Jaridar Blueprint tace kakakin majalisar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana cewa akwai yiwuwar jam'iyyar APC ta saki jadawalin tsarin shugabancin majalisar dattawa ta 10 bayan azumin Ramadan.

Sanata Basiru ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Laraba, yayin wata tattauna da gidan talbijin na Channels tv a shirin su mai suna Sunrise Daily.

Ga jerin ƴan majalisar da ke neman shugabancin majalisar dattawa ta 10:

1. Senator Jibrin Barau (Kano ta tsakiya).

2. Sani Musa (Niger ta Gabas).

3. Orji Kalu (Abia ta Arewa).

4. GodsWill Akpabio (Akwa-Ibom ta Arewa maso Yamma).

5. Senators Osita Izunaso (Imo ta Yamma).

6. Peter Ndubueze (Imo ta Arewa).

7. Abdul’Aziz Yari (Zamfara ta Yamma)

Kara karanta wannan

Zargin Ta'addanci: Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokoki a Arewa Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabo

8. Ahmad Lawan (Yobe ta Arewa).

9. Ali Ndume (Borno ta Kudu).

Atiku, Obi Da Sauran Masu Son Ganin An Tsige Tinubu

A wani rahoton na daban, kun ji yadda wasu ƴan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyun su ke neman kotu ta ƙwace nasarar Bola Tinubu.

Atiku da Peter Obi na jam'iyyun PDP da LP suna akan gaba wajen ganin kotu ta kwace nasarar da Tinubu ya samu ta lashe shugabancin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng