Gwamna Uzodinma Ya Ayyana Kudirinsa na Neman Tazarce a Jihar Imo

Gwamna Uzodinma Ya Ayyana Kudirinsa na Neman Tazarce a Jihar Imo

  • Gwamnan Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Hope Uzodimma, ya ayyana kudirin neman tazarce a zaben gwamna da ke tafe
  • A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 ne hukumar zaɓe ta ƙasa INEC zata gudanar da zaɓen gwamna a Imo da wasu jihohi 2
  • Uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ta yanke cewa bata da wani ɗan takara a jihar Imo face gwamna mai ci, Uzodinma

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sanar da shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) cewa ya aminta zai nemi tazarce zango na biyu kan kujerarsa a zaɓe mai zuwa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Gwamna Uzodinma ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga mambobin APC da suka haɗa da wakilan kwamitin gudanarwa na jiha, kananan hukumomi da gundumomi.

Kara karanta wannan

Neman Magajin Emefiele Ya Yi Nisa, An Hasko Wasu Manyan Mutane Da Tinubu Zai Iya Ba Mukamin

Gwamna Hope Uzodinma.
Gwamna Uzodinma Ya Ayyana Kudirinsa na Neman Tazarce a Jihar Imo Hoto: Hope Uzodinma
Asali: UGC

Yayin jawabinsa, wanda ya yi a Hedkwatar APC da ke Titin Okigwe a Owerri, babban birnin jihar Imo, gwamnan ya yaba wa mambobin jam'iyya bisa haɗin kan da suka gina.

Gwamna Uzodinma ya buƙaci baki ɗaya mambobin jam'iyyar APC da su ci gaba da ba da haɗin kai kuma su yi duk me yuwawa wjaen ƙara wa jam'iyya karfi da ƙima a wurin jama'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya faɗa musu cewa kuskuren da suka tafka a baya ya wuce an yafe musu, sannan kuma ya tunatar da su cewa, "Biyayya na da matuƙar muhimmanci ga jam'iyya, haka siyasa ta gada."

APC ta yanke wanda zata ba tikitin takara

A nasa jawabin ga dandazon 'ya'yan APC da suka halarci wurin, mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar kudu maso gabas, Dakta Ijeomah Arodiogbu, ya gode nusu bisa goyon bayansu.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Bayelsa

Bayan haka ya bayyana cewa:

"Uwar jam'iyya ta ƙasa ta amince babu tababa cewa gwamna Hope Uzodinma, shi ne kaɗai ɗan takarata na gwamna a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023."

An maye gurbin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Kogi

A wani labarin kuma Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus Saboda zargin hannu a ta'addanci

Majalisar dokokin jihar Kogi ta tsunduma cikin rikici bayan kammala zaben mambobinta a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamna Yahaya Bello ya aike wa majalisar da sunayen mambobi 9 da yake zargi da hannu a aikata ta'addanci ranar zaɓe, ciki har da shugaban masu rinjaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262