APC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Amince da Tsarin Kato Bayan Ƙato a Zaben Kogi
- Jam'iyyar APC ta sauya tsarin da zata yi amfani da shi a zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Kogi
- A wata wasiƙa da APC ta aike wa hukumar zaɓe INEC, jam'iyya mai mulki ta aminta da zaben kato bayan ƙato wajen fidda ɗan takara
- A ranar Jummu'a 14 ga watan Fabrairu, APC ta shirya gudanar da zaɓen amma ta ce zata ƙirga kuri'u washe gari
Kogi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta amince da tsarin kato bayan ƙato wajen gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a jihar Kogi.
Punch tace matakin sauya tsarin zaben daga amfani da Deleget zuwa zaɓen Kato bayan kato na kunshe ne a wata wasiƙa da muƙaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyari, ya rubuta.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Afrilu, an rubuta ta domin sanar da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) matakin da jam'iyyar APC ta ɗauka.
Kitimurmura: Kotu ta soke wasu tarukan zaben APC da aka yi a jihar Arewa don zabo dan takarar gwamna
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A rahoton Vanguard, Wani sashin wasiƙar ya ce:
"Dangane da takardarmu ta farko mai kwanan watan 25 ga watan Janairu, 2023, mai lamba APC/NHDQ/INEC/19/023/191, wanda muka sanar da hukumar INEC tsarin da zamu bi wajen fidda ɗan takarar gwamna a jihar Kogi.
"A yanzu, jam'iyyar mu mai albarka APC ta sake nazari kan matakan da zata yi amfani da su a zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a Kogi kuma ta amince ta koma tsarin kato bayan kato maimakon na Deleget da ta sanar a baya."
"Ranar zaben fidda gwanin na nan kamar yadda muka tsara watau ranar Jummu'a 14 ga watan Afrilu, 2023. Don haka zamu shirya taro na musamman don tantance ɗan takarar da ya samu rinjayen kuri'u ranar 15 ga watan Afrilu."
Tseren gaje kujerar gwamna Yahaya Bello ya ƙara daukar zafi bayan manyan kusoshin gwamnatin jihar Kogi sun lale miliyan N50m sun karɓi Fam ɗin takara a APC.
Daga cikinsu har da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Abdulkareem Asuku, Audita Janar, Ahmed Ododo da kwamishinan kananan hukumomi, Salami Ozigi-Deedat.
PDP ta kara shiga matsala a jihar Katsina
A wani labarin kuma Kotu Ta Rushe Sabon Kwamitin Shugabannin PDP Na Riƙo a Jihar Katsina
Babbar Kotun jihar Katsina ta tsige shugaban da sauran mambobinsa na kwamitin rikon kwarya, wanda PDP ta kafa su tafiyar da jam'iyyar a Katsina.
Asali: Legit.ng