Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Murabus Din Shugaban Jam'iyyar APC Na Ƙasa

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Murabus Din Shugaban Jam'iyyar APC Na Ƙasa

  • An shiga cikin halin rashin tabbas a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan murabus ɗin Abdullahi Adamu
  • Jita-jita ta yi ta yawo cece Sanata Abdullahi Adamu ya haƙura da shugabancin jam'iyyar ta APC
  • Sai dai jam'iyyar ta fito fili ta bayyana gaskiyar zance, inda tace har yanzu Abdullahi Adamu yana nan daram akan kujerar sa

Abuja - Batun jita-jitar murabus ɗin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanya fargaba a cikin jam'iyyar.

The Guardian tace jita-jitar na zuwa bayan mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa (yankin Arewa maso Yamma), Salihu Lukman, ya buƙaci ya yi murabus saboda ya kasa bayyana yadda aka kashe kudaɗen da da jam'iyyar ta tara.

APC ta musanta murabus din Abdullahi Adamu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Salihu Lukman ya bayyana cewa abinda yakamata shugaban yayi shine ya haƙura da shugabancin jam'iyyar, a ba kirista domin samar da daidaito kan tikitin muslim/muslim na jam'iyyar, cewar rahoton The Punch

Kara karanta wannan

Suna Dab Da Barin Mulki, Hadimin Shugaba Buhari Ya Yi Wa Shahararren Malamin Addini Kaca-Kaca

Sai dai binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa, Abdullahi Adamu baya ƙasar nan, yana ƙasar waje domin a duba lafiyar sa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani ƙusa a jam'iyyar wanda ya nemi da a sakaya sunan sa, ya ce ba abin mamaki bane idan jita-jitar murabus ɗin na Adamu ta zama gaskiya.

“Adamu kawai yayi tafiyar sa ne ba wanda ya gayawa daga cikin ƴan kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC). A yanzu da muke magana da kai, babu wanda ya san inda yake. Don haka idan an ce yayi murabus, waye ni da zance ba gaskiya bane?"

Jam'iyyar APC tayi watsi da jita-jitar

Da aka tuntuɓi kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, dangane da lamarin, ya yi watsi da jita-jitar a matsayin ƙanzon kurege ce.

“Babu wani abu makamancin wannan. Har yanzu Sanata Abdullahi Adamu shine shugaban jam'iyyar APC na ƙasa." A cewarsa

Kara karanta wannan

An Kunno Wa Fitaccen Ministan Buhari Wuta, Ana Neman Gwamnatin Tarayya Ta Cafke Shi

INEC Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta gayawa kotu dalilin da ya sanya Atiku Abubakar bai cancanci lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.

Hukumar zaɓen tace akwai ƙa'idoji da ɗan takarar na jam'iyyar PDP bai cika ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng