Rigima Ta Kunno Kai Tsakanin Gwamna Mai Barin Gado Da Magajin Sa a Benue

Rigima Ta Kunno Kai Tsakanin Gwamna Mai Barin Gado Da Magajin Sa a Benue

  • An tayar da jihohin wuya tsakanin gwamnan jihar Benue mai barin gado da wanda zai gaje sa
  • Zaɓaɓɓen gwamnan jihar ya yi fatali da wani sabon ƙudirin doka da gwamna Ortom zai aikewa majalisa
  • Hyacinth Alia ya yi kira ga al'ummar jihar da kada su yarda ƴan majalisun su su amince da wannan sabon ƙudirin

Jihar Benue- Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Benue, Fada Hyacinth Alia, ya sanya ƙafa yayi fatali da yunƙurin da gwamnan jihar mai barin gado, Samuel Ortom, yake yi na kafa wata sabuwar doka kan fansho.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alia, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya fara ƙoƙarin dakatar da yunƙurin kafa dokar ba gwamna Ortom fansho na dindindin.

Rigima ta kunno kai tsakanin Ortom da Alia
Zababben gwamnan Benue yayi watsi da sabon kudirin gwamna Ortom Hoto: Samuel Ortom, Hyacinth Alia
Asali: UGC

An samo cewa gwamnan yana shirin aikewa majalisar dokokin jihar ƙudirin sabuwar dokar domin tayi duba akai.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Duk Da Shugaba Buhari Ya Sako Kudi, ASUU Tace Akwai Sauran Rina a Kaba

Sai dai, da yake watsi da wannan sabon yunƙurin na gwamnan, Alia yayi kira ga mutanen jihar Benue da su sanya ƴan majalisar su dake wakiltar su a majalisar dokokin jihar su yi fatali da wannan ƙudirin dokar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa da Tersoo Kula, kakakin zaɓaɓɓen gwamnna ya fitar, ya bayyana cewa amincewa da wannan ƙudirin zai yiwa dukiyar jihar illa.

Sabon ƙudirin dokar a cewar sanarwar, yayi tanadin cewa bayan ranar 29 ga watan Mayu, za a ba Ortom damar tafiya da wasu kadarorin gwamnati waɗanda suka kwanta masa a rai a matsayin ladan wahaltawa jihar da ya yi.

Sanarwar na cewa:

“A cewar ƙudirin, za a ginawa gwamna Ortom irin danƙareren gidan da yake so a ko wane ɓangare ne na ƙasar nan inda ya zaɓi ya cigaba da rayuwa bayan ya bar mulki"

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan APC Ya yi Kus-Kus Da Shugaba Buhari, Ya Ce Jiharsa Na Neman Dauki

“Gwamnatin jihar ita zata riƙa biyan kuɗin tafiye-tafiyen sa zuwa dubo lafiyar sa da ta iyalan sa, tare da kuma wasu maƙudan kuɗaɗe da za a riƙa biyan sa a kowane wata."

A cewar kakakin, ƴan majalisar dokokin jihar sun gindaya wa gwamnan wani sharaɗi kafin su amince da wannan ƙudirin dokar.

Sai dai, kakakin shugaban majalisar dokokin jihar, Wuese Orshi, ya musanta zargin inda ya bayyana shi a matsayin soki burutsu ne kawai.

Ana Neman Gwamnatin Tarayya Ta Cafke Fitaccen Ministan Buhari

A wani labarin na daban kuma, an nemi Antoni Janar na tarayya da ya cafke ministan Buhari kan kalaman da ya jefi Peter Obi da su.

Ministan watsa labarai da al'adu, Lai Mohammed, yayi wasu zarge-zarge akan Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng