APC Ta Kori Sanata Da Aka Zaba A Karon Farko, Ta Bada Kwararan Dalilai

APC Ta Kori Sanata Da Aka Zaba A Karon Farko, Ta Bada Kwararan Dalilai

  • Jam'iyyar APC reshen Jihar Taraba ta kori sanata wanda ya ci zabensa karo na farko, David Jimkuta, wanda zai rika wakiltan Taraba ta Kudu a majalisa ta 10
  • APC ta karamar hukumar Takum ce ta sallami Jimkuta a jihar kan zargi masu alaka da yin ayyukan cin amanar jam'iyya
  • A wata wasikar korar mai dauke da sa hannun ciyaman din APC na jihar 7 ga watan Afrilu, an kori Jimkuta bayan rahoto kwamitin ladabtarwa a kansa

Jihar Taraba - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta kori, David Jimkuta, zababben sanata mai wakiltar mazabar Taraba ta Kudu a majalisa zubi na 10.

The Tribune ta rahoto cewa jam'iyyar na APC a karamar hukumar Takum na jihar Taraba ta kori Jimkuta ne kan zarginsa da ayyukan cin amanar jam'iyya.

Kara karanta wannan

Ta leko, ta koma: APC ta kori zababben sanata kwanaki kadan bayan ya lashe zabe

Dan takara
APC Ta Kori Sanata Da Aka Zaba A Karon Farko, Ta Bada Kwararan Dalilai. Hoto: APC Nigeria
Asali: UGC

An sanar da korar sanatan da aka zabe shi a karon farko ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Afrilu dauke da sa hannun Honarabul Sirajo Sallau, shugaban APC na Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba.

Wasikar ta yi bayani cewa an dauki matakin korar zababben sanatan ne saboda tattaunawa da aka yi kan rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa a kansa ta bada bayan zargin da aka yi wa Jimkuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta cigaba da bada bayani dangane da ayyuka uku na cin amanar jam'iyya da aka samu Jimkuta da laifin aikatawa, sune:

1. Jimkuta ya dauki nauyi kuma ya yi wa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta jihar Taraba kamfe da dan takarar gwamnanta.

2. Zababben sanatan a fili ya nesanta kansa tare da watsi da dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress, APC a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jam'iyyar APC ta kori wani fitaccen sanata a jihar Arewa

3. An same shi da laifin nema wa jam'iyyar PDP kuri'u da dan takarar gwamnan ta yayin zaben gwamna.

Kefas Agbu na jam'iyyar PDP ne ya kayar da jam'iyyar APC a zaben na ranar 18 ga watan Maris.

An ayyana Agbu a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri'u 302,614 inda ya kada Muhammad Yahaya na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, wanda ya samu kuri'u 202,277.

Lokacin Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi, Kalu

A wani rahoton mai alaka da wannan, Sanata Orji Kalu, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya ya sanar da niyyarsa na shiga takarar shugabancin majalisar tarayya zubi na 10.

Kalu wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar, ya furta hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164